✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojojin Nijar sun kama dan ta’adda Baleri, uban gidan Bello Turji

An kama Baleri wanda mai gidan Bello Turji ne a lokacin da shi da yaransa ke shirin kai hari a yankin Maradi da ke Jamhuriyar…

Sojojin hadin gwiwa sun kama Beleri, kasurgumin dan bindigar Najeriya da ake nema ruwa a jallo a Najeriya.

Baleri uban gida ne ga kasurgumin dan bindiga Bello Turji, wand ya addabi al’ummar yankunan Jihar Zamfara da hare-haren ta’addanci da kuma satar mutane domin karbar kudin fansa.

Baleri wanda shi ma ɗan Zamfara ne ya jima yana addabar al’ummar jihar da ma wasu yankunan Nijar, musamman jihar Maradi.

Shi ne na 40 a jerin ’yan ta’adda da hukumomin Najeriya ke nema ruwa a jallo, har ta yi alkawarin lada mai tsoka ga duk wanda ya taimaka aka kamo shi.

Sojojin na Nijar sun sanar cewa an kama Beleri ne a garin Rigar Kowa Gwani da ke yankin Gidan Rumji na jihar Maradi a kasarsu.

Rundunar sojin Nijar ta ce dakarun Runduna ta Musamman mai suna Farautar Bushiya sun yi nasarar kama Beleri ne da misalin jarfe 1 a kan iyakar kasashen biyu,  a jihohin Zamfaran Najeriya da kuma Maradin Jamhuriyar Najeriya.

An kama shi ne a lokacin ya yake tsaka da  ganawa da yaransaa shirinsu na kai hari a Najeriya da Nijar.