✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sojoji sun kwace bindigogi 517 a Filato da Kaduna

Sojoij sun kashe ’yan bindiga, sun tsare wasu tare da gurfanar da mutanen da ake zargi da haddasa rikice-rikice a gaban kotu

Sojoji sun kama bindigogi akalla 517 daga hannun bata-gari a cikin dan takaitaccen lokaci a Jihar Filato da sassan jihohin Kaduna da Bauchi.

Makaman da sojojin rundunar soji ta Operation Safe Haven suka kama sun hada bidigogi 47 masu sarrafa kansu — AK-47 guda 27 da SMG daya da G3 uku da FN rifle daya da Barretta biyu da Harris Burg pistol daya da kuma Beretta pistol shida.

Sojojin sun kuma kama makamai gudan 477 kirar gida: “Rifle guda 183 da bindigar harbi-ruga 163 da Pistol 102 sai SMG guda 19 da Pump action 1 da kuma single Barrel guda shida,” kamar yadda Kwamandan rundunar kuma Babban Kwamandan Rundar Soji ta 3, Manjo Janar Ibrahim Ali ya sanar.

Ya bayyana cewa rundunar ta Operation Safe Haven da ke aiki a JIhoihn Filato da Bauchi da kuma Kaduna ne suka kwace bindigogin a samamen da suka kai a wurare daban-daban a jihohin.

Manjo Janar Ali ya sanar da haka ne a lokacin da yake mika makaman ga Kodinetan Cibiyar Yaki da Yaduwar Makamai ta Kasa, Manjo Janar Hamza Bature a hedikwatar rundunar da ke Jos, ranar Alhamis.

Ya bayyana cewa rundunar ta kuma yi nasarar kama wasu mutane da ke tayar da fitintinu a jihohin, a matsayin wani bangare na aikinta domin dakile kashe-kashe da yaduwar makamai ba bisa ka’ida ba a tsakanin jama’a.

“Mun kuma hallaka ’yan bindiga da dama, mun tsare wadanda ake zargi tare da gurfanar da mutanen da ake zargi da haddasa rikice-rikice a gaban kotu,” inji shi.

Da yake jawabi, Kodineton Cibiyar, ya bukaci rundunar da ta kara azama wajen kara ganowa da kuma kwace sauran haramtattun makaman da ke hannun mutane, musamman ganin cewa ana kara tunkarar lokacin babban zabe mai zuwa.

Ya jinjina wa rundunar tare da yi wa dakarunta fatar samun karin nasara a kan aikinsu.