Sojojin Rundunar Operation SAFE HAVEN, sun kama wasu ƙasurguman ’yan bindiga biyu, tare da ƙwato alburusai a yankin Rafiki da ke Ƙaramar Hukumar Bassa, a Jihar Filato.
Sun kama shugabannin ’yan ne a ranar Laraba.
- Babban layin lantarkin Najeriya ya faɗi karo na 11 a 2024
- Yadda aka kama gungun barayin motoci a Sakkwato
Rundunar ta bayyana cewa samamen na cikin ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya a lokacin bukukuwan ƙarshen shekara.
Kakakin rundunar, Manjo Samson Zhakom, ya ce an kama mutanen ne yayin wani samame da suka kai biyo bayan bayanan sirri da suka samu.
Ya yi jawabi yayin baje-kolin masu laifi a garin Jobs.
“Sojoji sun kama waɗanda ake zargi, Mohammed Musa wanda aka fi sani da Mamman, tare da abokinsa Mallam Alhassan Samaila.
“A lokacin samamen, an ƙwato harsasai guda 439, waɗanda suka ɓoye a cikin jarka mai ɗaukar mai lita huɗu.”
Manjo Zhakom, ya ƙara da cewa bincike ya nuna cewa waɗanda aka kama suna fakewa da aikin direbobin mota don yi wa ’yan bindiga safararr makamai a Jihohin Filato, Kaduna, da Zamfara.
Ya ce waɗanda ake zargin na bayar da bayanai masu amfani yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike don kama sauran mambobin ƙungiyarsu tare da ƙwato sauran makamansu.
Kakakin, ya tabbatar da cewa rundunar tana ci gaba da aiki don kare rayuka da dukiyoyin jama’a a Jihar Filato.