Sojojin Najeriya da ke rundunar tsaro ta Operation Hadin Kai sun harbe wasu ’yan ta’addan Boko Haram da ISWAP da ke kokarin tsallakowa Najeriya daga Jamhuriyar Kamaru.
’Yan ta’addan, wadanda suka kai biyar dai, a cewar sojoji sun kwashi kashinsu a hannu ne sakamakon wasu bayanan sirri da aka samu.
- Bidiyon Dala: APC ta bukaci Ganduje ya yi watsi da sammacin Muhuyi
- Threads: Abubuwa 5 da ya kamata ku sani a kan sabuwar kishiyar Twitter
Sabon Daraktan Yada Labarai na Hedkwatar Tsaro, Manjo Janar ES Buba, ne ya bayyana haka a hedkwatar tsaro da ke Abuja, ranar Alhamis.
Ya ce sun yi wa ’yan ta’addan kwanton bauna ne a kan hanyar Bula Yobe zuwa Darel Jamel a Karamar Hukumar Bama ta Jihar Borno.
Ya kuma ce dakarun sun sami nasarar cafke wasu ’yan ta’addan su 10 da ransu.
Buba, wanda mataimakinsa, Birgediya Janar Abdullahi Ibrahim ya wakilta, ya ce sun kuma kama makamai masu yawa daga hannun ’yan ta’ddan.
Daga cikin kayayyakin ya ce har da buhun fulawa da na omo, sannan kuma an kama masu hada baki da su.