Dakarun sojojin Najeriya karkashin rundunar Operation Hadarin Daji sun harbe wasu ’yan ta’adda a kauyen ’Yar Tasha da ke Karamar Hukumar Maru ta jihar Zamfara.
Sun gamu da ajalin nasu ne lokacin da suke tsaka da girbin amfanin gona a gonar wasu manoma a yankin.
- Nan da sati 3 jirgin kasan Abuja-Kaduna zai dawo aiki
- NDLEA ta kama makaho dan Nijar da safarar miyagun kwayoyi
Sojojin sun kuma kashe wani kasurgumin dan bindiga mai suna Bada, wanda rahotannin suka ce ya kai hari kasuwar kauyen sannan ya kashe wasu manoma kafin ya fara girbe musu amfanin gonar.
Daraktan Yada Labarai na Hedkwatar Tsaro ta Kasa, Manjo-Janar Musa Danmadami ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da safiyar Litinin, ya kuma ce sojojin sun kwato babur da wasu makamai da ma wasu kayayyaki masu yawa.
Danmadami ya kuma ce an hori dakarun da su ci gaba da ragargazar ’yan ta’addan tare da ganin burinsu na tarwatsa zaman lafiyar kasa bai cika ba, tare da ba dakarun isassun bayanan da za su taimaka musu.
Daraktan ya kuma ce sojojin sun kuma kai farmaki kan ’yan ta’adda a kauyukan Gamraki da Kwatarkwashi da ke Karamar Hukumar Bungudu ta jihar Zamfaran, sannan suka kwato wasu mutum biyu da aka sace.
Ya kuma ce, “A kauyukan, sojojin sun farmaki mutanen da suka sace wasu mutum biyu, inda suka yi musayar wuta da su sannan suka kwato mutanen da aka sace, suka kashe dan ta’adda daya, wasu da dama kuma suka gudu da raunuka a jikinsu.
“Sojojin sun kuma kwato wata bindiga kirar AK-47 guda daya, da wata mai kirar jigida guda daya sai kuma kunshin albarusai guda biyu,” inji shi.