Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta hallaka ’yan ta’adda biyar tare da ceto wasu mutum 78 da aka sace a wani samame da dakarunta suka kai a Jihar Borno.
Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Manjo Janar Onyema Nwachukwu ne, ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, a Abuja.
- ’Yan bindiga sun sace fasinjoji 10 a Benuwe
- Yadda labaran karya suka kusa kashe min aure — Lai Mohammed
Nwachukwu, ya ce sojojin na ci gaba da kai hare-hare kan ’yan ta’adda a Arewa maso Gabashin Najeriya.
A cewarsa sojojin sun yi nasarar kai hare-hare tare da kwato kauyuka shida da ‘yan ta’adda suka kwace, bayan wani kazamin artabu da suka yi.
Ya ce, kauyukan da sojojin suka kwato sun hada da Ngurusoye, Sabon Gari, Mairamri, Bula Dalo, Bula Dalo tsawo, Yamanci da kuma Gargaji.
Ya ce dakarun sun kwato wasu kayayyaki da suka hadar da tutar ’yan ta’addan da kuma wayar hannu.
“Wadanda aka ceto suna tsare ne domin gudanar da bincike a kansu, kafin kuma a bayyana sunayensu.
“Sojojin na ci gaba da kai hare-haren kawar da ’yan ta’adda da masu tayar da kayar baya a Arewa maso Gabas,” in ji shi.