✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun hallaka ’yan ta’adda 28 a Yobe

Mayakan Boko Haram sun kwashi kashinsu a hannu bayan sun yi wa sojoji kwanton bauna

Dakarun sabuwar rundunar tsaro ta Operation Tura ta Kai Bango, wani sashe na rundunar tsaro ta Operation Lafiya Dole sun hallaka ’yan kungiyar Boko Haram a Karamar Hukumar Gujba ta Jihar Yobe.

Mukaddashin Daraktan Watsa Labarai na Shalkwatar Tsaro ta Kasa, Birgediya Benard Onyeuko ne ya bayyana hakan a wata sanarwa ranar Lahadi.

Ya ce dakarun sun yi nasarar ne bayan wani kwanton baunar da ’yan ta’adda suka yi musu amma suka ragargaje su da manyan makamansu.

Benard ya ce sojojin sun yi amfani da kwarewarsu wajen dakile mayakan, lamarin da ya jawo musu tafka mummunar asarar mutane.

A cewarsa, “A sakamakon karon-battar da aka yi da, mun hallaka mayakan Boko Haram 28, yayin da wasu da dama kuma suka tsere da munanan raunuka a jikinsu.

“Bugu da kari, mun lalata wata motar yaki ta Boko Haram da mutanen da ke cikinta, sannan muka cafke wasu da ke kokarin guduwa.

“Makaman da muka kwace daga hannunsu sun hada da wasu bindigogin harbor jirage guda biyu, bindigogi kirar AK47 guda 13, da wasu manyan bindigogi hudu sai kuma injin sarrafa su,” inji shi.

Sai dai ya ce soja daya ya samu rauni sakamakon ba-ta-kashin, kuma tuni aka garzaya da shi asibitin sojoji inda yake ci gaba da samun kulawa.

Daga nan sai ya kara ba wa mutanen yankin Arewa maso Gabas tabbacin cewa Rundunar na murkushe ’yan ta’addan daga yankin baki daya.