✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji Sun Hallaka ’Yan Bindiga 7 Sun Kwato Makamai A Kaduna

Rundunar Sojin Najeriya ta daya da ke jihar Kaduna, ta ce dakarunta sun kashe wasu ’yan bindiga guda bakwai. Rundunar ta ce ta yi nasarar…

Rundunar Sojin Najeriya ta daya da ke jihar Kaduna, ta ce dakarunta sun kashe wasu ’yan bindiga guda bakwai.

Rundunar ta ce ta yi nasarar kwato makamai da babura daga wurin ’yan ta’addar ranar Lahadi.

Mukaddashin Daraktan Hulda da Jama’a na rundunar, Laftanar Kanal Musa Yahaya ya bayyana wa Kamfanin Dillacin Labaran Najeriya (NAN) a Kaduna cewa,“ Dakarun da aka tura a hanyar Udawa zuwa Kurebe a ranar Lahadi 19 ga watan Mayu sun yi ba ta kashi da ’yan bindiga.

“Sojoji sun yi wa ’yan ta’addar luguden wuta mai tsanani da ta kai ga halaka ’yan ta’adda biyar, suka  kwato bindiga daya, harsashi shida, da sauran kayayyaki.”

Ya ce, su kuma dakarun rundunar da aka tura a Sabon Birni a karamar hukumar Igabi ta jihar sun kama wasu da ake zargin ’yan ta’adda ne a yankin Baka a ranar 19 ga Mayu, 2024.

Yahaya ya ce, “Sun kwato bindiga kirar AK 47 daya da babura biyu yayin da wasu daga cikin ’yan bindigar suka tsere da manyan raunuka.”

Ya kuma bayyana cewa sojojin rundunar a kauyen Kwaga da ke karamar hukumar Birnin Gwari sun yi nasarar kashe biyu daga cikin ’yan ta’addar yankin.

A can ma, Yahaya ya ce, sun kwato bindigogi kirar AK 47 guda biyu.

Kakakin rundunar ya ce babban kwamandan runduna ta daya kuma kwamandan Operation, Whirl Punch, Manjo janar Mayirenso Saraso ya  yaba wa sojojin bisa kwazon da suka nuna.

Ya yi kira ga ’yan Najeriya da su rika kai rahoto da bayanan sirri ga sojoji da sauran jami’an tsaro domin daukar matakan da suka dace cikin gaggawa.