Akalla ’yan bindiga 120 ne suka gamu da ajalinsu sakamakon ruwan wutar da jiragen yakin sojojin saman Najeriya suka yi musu a dajin Sububu da ke Jihar Zamfara.
Kafar yada labarai ta PRNigeria ta rawaito cewa an karkashe su ne a wasu hare-haren da aka kai ta sama ranar Litinin, bayan wasu makwabtan yankin sun kai rahoton sirri kan shige da ficen bata-garin a dajin.
- An fara gyaran makabartar Gashuwa da ruwa ya yi wa barna
- Za a fara daure barayin akwatin zabe shekara 20
Wani jami’in leken asiri ya shaida wa majiyar tamu cewa sai da jiragen yakin suka gama nazartar dajin da kuma kaiwa da komowar ’yan bindigar kafin su fara yi musu ruwan wuta.
“Bayan samun rahotannin sirri ranar 12 ga watan Yulin 2021 cewa wani gungun ’yan bindiga na hada ayari a dajin Sububu da Jajani da kuma Dammaka, an girke jirgin yaki domin ya yi nazari kafin kaddamar da harin.
“Hakan ta sa jirgin ya gudanar da shawagi sannan ya gano gungun ’yan bindigar na shigowa suna yin sansani a dajin a karkashin wasu manyan bishiyoyi na dajin.
“Daga bisani ne aka yi musu dirar mikiya aka kuma cim musu; Kadan daga cikinsu da suka tsira da rai an gan su suna kokarin ranta a na kare.
“Ana kiyasin cewa an kashe sama da 125 daga cikinsu, bisa bayanan da muka tattara daga yankin,” inji jami’in.
Da majiyar tamu ta tuntubi kakakin Rundunar Sojin Sama na Najeriya, Eya Kwamando Edward Gabkwet, ya tabbatar da harin tare da cewa sun kuma lalata baburan ’yan bindigar.
To sai dai bai yi karin bayani kan hakikanin yawan wadanda aka kashe ba.
Sojojin Najeriya karkashin rundunar Operation Hadarin Daji wacce ta kunshi sojoji da sauran jami’an tsaro ita ce dai a yanzu take yaki da ’yan bindiga a yankin Arewa maso Yammacin kasar.