Shalkwatar Sojojin Najeriya ta ce dakarun rundunar tsaro ta Operation Tura ta Kai Bango a ranar Talata sun hallaka wasu manyan kwamandojin Boko Haram biyu da ake nema ruwa a jallo.
Sojojin sun ce an hallaka Abul-Bas da Ibn Habib ne a wata karon-batta da suka yi da su a yankin Pulka na jihar Borno.
- Sulhu da ’yan bindiga: Dalilin da Gumi da El-Rufa’i suka yi hannun riga
- Nau’ukan abinci da ya kamata masu cutar sankara su daina ci
Daraktan Sashen Watsa Labarai na rundunar, Birgediya Janar Mohammed Yarima ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a Abuja ranar Asabar.
Yarima ya ce zafafa kai hare-haren da dakarunsu suke yi karkashin jagorancin Operation Lafiya Dole ya yi matukar illa ga kungiyoyin Boko Haram da na ISWAP da suka addabi yankin Arewa maso Gabas.
Ya ce dakarun runduna ta 121 da na bataliya ta 151 ranar Talata sun yi wani kwanton bauna a kan wata mahadar garuruwan Vuria da Guja dake kan hanyar Banki zuwa Pulka a jihar Borno.
Kakakin ya ce sun sami nasarar hallaka mayakan kungiyar guda uku, ciki har da kwamandojin da ake nema ruwa a jallo guda biyu.
Yarima ya ce sun kuma kwato manyan bindigogi guda uku, masu kirar AK47 guda bakwai, harsasai guda 446, babur kirar Boxer da kuma wata wayar salula guda daya.
“Mun jima muna tattara bayanan sirri a kan wadannan ’yan ta’addan guda biyu dake da sansani a dajin Sambisa.
“Abdul-Bas babban kwamanda ne dake taimakawa Abu Fatima, yayin da shi kuma Ibn Habib kwamandan Boko Haram ne dake kula da sansanonin Njima da Parisu a dajin Sambisa,” inji shi.