✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sojoji sun hallaka kasurgumin dan bindigar Zamfara, Alhaji Auta

Dan bindigar dai na daga cikin wadanda suka addabi yankin.

Sojojin Najeriya a ranar Asabar sun hallaka kasurgumin dan bindigar nan da ya addabi yankin Birnin Magaji na Jihar Zamfara, Alhaji Auta.

Kazalika, sojojin sun kuma hallaka mambobin da ke cikin gungunsa, yayin wasu hare-hare da suka kai ta sama, lokacin da ’yan bindigar ke tsaka da jimamin kisan nashi.

An dai hallaka mambobin ne a sansaninsu da ke kauyen Jama’are Bayan Dutse da ke gundumar Nasarawa Mailayi.

Majiyoyi da dama sun tabbatar wa Aminiya labarin kisan na Alhaji Auta, ko da yake sun ce ba za a iya tabbatar da yawan mutanen da aka kashe ba.

Dan bindigar dai na daga cikin wadanda suka hana jama’ar yankin sakat.