Dakarun Sojin Najeriya tare da hadin gwiwar ’yan sanda sun lalata maboyar ’yan bindiga tare da ceto wasu mutum hudu a Karamar Hukumar Yorro a Jihar Taraba.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mukaddashin daraktan hulda da jama’a na rundunar, Laftanar Olabodunde Oni, ya fitar a ranar Lahadi.
- Tsohon gwamnan Yobe, Bukar Abba, ya rasu a Saudiyya
- INEC ta dakatar da jami’inta kan batan sakamakon zabe a Filato
Ya bayyana cewa sun tarwatsa maboyar ’yan bindigar da suka addabi yankin Yorro da kewaye.
Ya ce sojojin sun yi arangama da ’yan bindiga a tsaunin Gampu da yankin Ban Yorro, inda suka yi wa ’yan ta’addan ruwan wuta.
“Har yanzu ana ci gaba da gudanar da aikin ceto wadanda aka sace a yankin tare da hada su da iyalansu.
“Rundunar soji ta jadadda aniyar tabbatar da tsaron lafiyar ’yan kasa da kuma tarwatsa masu aikata laifuka a jihar nan.
“An yi kira ga jama’a da su bai wa sojoji goyon baya ta hanyar bayar da sahihan bayanai don taimakawa wajen inganta tsaro.”