✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sojoji sun dakile wani sabon hari a Sakkwato

Dakarun sun dakile harin bayan samun bayanan sirri.

Rahotanni da ke fitowa daga Jihar Sakkwato sun bayyana cewa dakarun soji sun dakile wani hari da ‘yan bindiga suka yi yunkurin kai wa a garin Goronyo.

Bayanai sun ce ‘yan bindigar sun tare hanyar da ‘yan kasuwa ke amfani da ita duk mako zuwa garin Goronyo cin kasuwa a ranar Lahadi.

“Sun tare titi da safe da nufin sace ‘yan kasuwa da kuma yi musu fashin kayayyakinsu.

“Amma dakarun soji sun dakile yunkurinsu bayan samun bayanai da suka yi,” cewar shugaban kasuwar Goronyo, Abdulwahab.

A makon da ya gabata wasu mahara sun tare hanyar kasuwar, inda suka kashe mutane da dama tare da sace wasu.

Kasuwar Goronyo kasuwa ce da ke ci duk sati, a gabashin jihar Sakkwato, amma ‘yan bindigar sun addabi mutanen da ke cin kasuwar duk mako.

Idan ba a manta ba a shekarar da ta gabata, mahara sun kashe ‘yan kasuwa da dama daga yankin.