✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun dakile harin mayakan ISWAP a Monguno

Dakarun Rundunar Hadin Gwiwa ta Kasa da Kasa (MNJTF) sun yi nasarar dakile wani harin mayakan ISWAP kafin wayewar garin ranar Litinin a yankin Monguno…

Dakarun Rundunar Hadin Gwiwa ta Kasa da Kasa (MNJTF) sun yi nasarar dakile wani harin mayakan ISWAP kafin wayewar garin ranar Litinin a yankin Monguno na Jihar Borno.

Rahoton da muka samu ya nuna ’yan ta’adan sun sha ragargaza ne a lokacin da suka kai wa garin hari cikin jerin gwanon motoci da babura da misalin karfe 1:30 na dare, ranar ta Lahadi.

Wasu majiyoyin leken asiri sun shaida wa Zagazola Makama, wani kwararre a fannin yaki da tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a Tafkin Chadi, cewa sojojin sun fatattaki mayakan ne  bayan kazamin fada har zuwa misalin karfe 2:30 na dare.

Sai dai majiyoyin ba su bayyana adadin mayakan da aka kashe a fadan ba.

Amma sun yi imanin cewa harin na ramuwar gayya ne ga kisan da rundunar ta yi wa ’yan kungiyar ta ISWAP a farmakin da sojoji suka kai a yankunan Sabon Tumbum da Jibularam da ke Karamar Hukumar Marte a kwanan nan.

Majiyar ta bayyana cewa, a ranar 1 ga watan Yuli da misalin karfe 10 na dare, manyan shugabannin ISWAP a cikin jerin gwanon wasu motoci 25 kirar Hilux, daga bangaren Kwalaram, suka isa Sabon Tumbu domin kwashe wadanda suka mutu da kuma wadanda suka jikkata suka nufi hanyar Daban Gajere.

“Wadanda suka mutu daga baya an dauke su zuwa kan iyakar Kekeno da Barwati a Karamar Hukumar Kukawa, inda aka binne su daga bisani ne maharan suka sake hada kansu.

“Haka nan mayakan da ke Dajin Arge kafin su ci gaba da kai farmaki a garin Monguno, suma sai da suka hada kansu,” inji majiyoyin.

A ranar 18 ga watan Yuni, ISWAP ta kai hari a garin Monguno, inda ta kashe jami’an rundunar hadin gwiwa ta farar hula uku tare da yin garkuwa da ma’aikatan agaji uku.

Monguno wanda ke da nisan kilomita 135 daga Maidugiri babban birnin Jihar Borno, yana da gidaje fiye da 154,000 na ’yan gudun hijira, kuma yana yawan fuskantar hare-hare ISWAP da Boko Haram.

Ko a ranar Asabar da ta gabata ma sai da wasu mayaka suka yi yunkurin kai hari ga sansanonin kungiyar agaji ta kasa da kasa (RCI).