✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Borno: Sojoji sun dakile mahara a garin Auno

Sojojin sun yi aune sannan suka fatattaki marahan.

Sojoji da ke sintiri a kan Babbar Hanyar Maiduguri zuwa Damaturu ta dakile wani hari da ’yan bindiga suka kai sansaninsu da ke garin Auno, Jihar Borno.

Wani ganau a Auno ya ce maharan a cikin jerin motoci hudu sun yi kokarin yi wa sojojin ba-zata, amma dakarun suka fatattake su.

“Sun buya a bayan wasu motoci masu zuwa daga Damaturu wanda aka bincika a kan hanyar.

“Wasu daga cikin sojojin da aka girke a daji kusa da wurin binciken ababen hawa sun hangi maharan amma saboda rashin masaniya daga shugabanninsu, sai suka yi ta harbi a sama. Maharan sun shige cikin daji yayin da suka ga ruwan harsasai,” a cewarsa.

Kazalika, ya ce sojojin sun kasance cikin shiri don gudun abin da ka iya zuwa ya dawo.

A watan Afrilu wasu mahara sun kai harin ba-zata a wani sansanin sojoji da ke kusa da garin Mainok, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da yawa.