Sojojin Najeriya da aka tura a garin Mafa sun yi nasarar dakile wasu hare-haren da ’yan ta’addan ISWAP suka kai kauyen Ajiri da ke Karamar Hukumar Mafa a Jihar Borno.
Bayanai sun ce wani kwamandan kungiyar ta ISWAP mai suna Abou Mubammed ne ya shirya harin wanda bai yi nasara ba.
- Gobara ta lakume rayuka biyu da gidaje 500 a Borno
- An kama mutumin da ya yi barazanar gayyatar ’yan awaren IPOB zuwa Legas
Wakilinmu ya ruwaito cewa, ISWAP ta shirya harin ne a matsayin martanin kashe mayakanta 41 da dakarun Operation Hadin Kai suka ka yi a makon da ya gabata, bayan sun kai wa matsugunansu hari a Mukdolo a ranar 26 ga Maris.
Zagazola Makama, kwararre a fannin yaki da tayar da kayar baya, kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi, ya ruwaito cewa, a taron da suka yi a Kajeri Dogumba da Bula Yagana Aliye a yankin na Mafa, mayakan ISWAP sun sha alwashin daukar fansa kan kisan gillar da aka yi wa mambobinsu.
An ce ‘yan ta’addan sun fara mamaye garin ne tun a daren Laraba, 29 ga Maris, 2023, inda suka yi yunkurin kai hari a sansanin soji wanda diga bisani aka yi artabu tsakanin bangarorin biyu har aka kai ga fatattakar su.
Ya ce daga baya sojojin sun fatattaki ‘yan ta’addan a wani artabu da suka yi da su tare da samun nasarar dakile harin, yana mai cewa “sun yi musu mummunar barna.”
Majiyar ta ce sakamakon haka ne ’yan ta’addan suka sake kai wani hari na kwantan bauna kan tawagar sojojin, amma suka fuskanci tirjiya har ta tilasta wa ’yan ta’addan tserewa.
Rahotanni na cewa daya daga cikin jami’an sa-kai na Civilian JTF ya jikkata a wannan arangama da aka yi yayin da ’yan ta’addan da dama suka jikkata.