Rundunar Sojin Jamhuriyar Dimokuraɗiyya Kongo ta ce ta daƙile juyin mulkin da wasu ’yan ƙasar da na ƙetare suka yi yunƙurin yi wa Shugaba Felix Tshikedi a Kinshasa, babban birnin ƙasar.
Rundunar ta ce an yi yunkurin kifar da gwamnatin kasar ne da sanyin safiyar ranar Lahadi a kofar gidan Ministan Kula da Tattalin Arziki da ke yankin Gombe, inda nan ne ofishoshin shugaban kasar suke.
- Makafin Dala: Garin naƙasassu da kowa ke ta kansa
- Nijar, Mali da Burkina Faso za su kafa sabuwar ƙungiya
Cikin wani jawabi da ya fitar ta gidan talbijin na ƙasar, mai magana da yawun sojojin ƙasar, Burgediya Janar Sylavin Ekenge, ya ce a yanzu ƙura ta lafa, kuma sojojin ƙasar na tsare da wasu da ake zargi da hannu a lamarin.
Jawabin nasa na zuwa ne sa’o’i bayan da wasu mutane ɗauke da makamai suka afka gidan tsohon shugaban ma’aikata kuma babban aminin shugaban ƙasar, da safiyar ranar Lahadi.
Shaidu sun ce ga wasu mutane kimanin 20 sanye da kayan sojoji sun afka wa gidan sannan suka ji ƙarar harbe-harben bindiga.
Kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ce maharan mambobin wata ƙungiya ce da ake kira ‘New Zaire Movement’ mai alaƙa da ɗan siyasar ƙasar da ke zaman gudun hijira a ƙetare, Christian Malanga.
Harin ya yi sanadiyyar mutuwar ’yan sanda biyu da ke gadin gidan da mahari guda kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito.
Kawo yanzu shugaban ƙasar Felix Tshisekedi bai ce komai ba game da batun.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na X da aka fi sani da Twitter a baya, Jakadan ƙasar Japan a Kinshasa, Kidetoshi Ogawa ya ce ministan bai samu rauni ba a harin da aka kai.
Tuni dai Jakadun ƙasashen ƙetare a kasar suka fara bukatar ’yan kasarsu da kaurace wa yankin da lamarin ya faru.