Dakarun Operation Hadin Kai sun kara ceto wata dalibar Makarantar Chibok, Yana Pogu, tare da tagwayen da ta haifa a hannun ’yan Boko Haram a Jihar Borno.
Sojojin tare da hadin gwiwar rundunar ’yan sakai ta CJTF sun ceto Yano Pogu ne a ranar Alhamis bayan sun kai farmaki a yankin Bula Dawo da ke Karamar Hukumar Bama a Jihar Borno inda suka kashe ’yan ta’adda da ba a tantance adadinsu ba tare da jikkata wasu da dama.
- Najeriya @62: Jawabin Buhari ga ’yan Najeriya takaicce
- Yadda manoma 14 suka rasu a hatsarin kwalekwale a Taraba
“A yayin arangamar, sojoji sun yi nasarar ceto Yana Pogu, dalibar Makarantar Chibok, wadda ita ce ta 19 a jerin daliban da Boko Haram ta yi garkuwa da su, tare da ’ya’yanta hudu,” in ji majiyar tsaro ta Zagazola.
Zagazola, wanda masanin tsaro kuma mai sharhi kan ta’addanci a yankin Tafkin Chadi ne, ya ce, sojojin sun tarwatsa wani sansanin ’yan ta’adda inda suka kashe dimbin ’yan ta’adda tare da fatattakar wasu da dama.
Ya ce, “An sami Yana dauke da wasu tagwaye ’yan watanni hudu a cikin wani yanayi mara kyau.
“Wasu daga cikin ’yan ta’addan da suka tsere sun yi yunkurin yi wa dakarun nasu kwanton bauna amma sojojin sun mayar da martani cikin gaggawa, lamarin da ya tilasta musu tserewa.
“An ceto karin wasu mata kuma an mika su ga Rundunar Sojin Kasa ta Brigade 21 Armored da ke Bama domin kula da lafiyarsu,” inji majiyar.
A watan Afrilun 2014 ne mayakan Boko Haram suka yi garkuwa da dalibai mata sama da 200 yawancinsu Kiristoci masu shekaru 16 zuwa 18 a Makarantar Sakandaren ’Yan Mata ta Gwamnati da ke Chibok, Jihar Borno.