Dakarun rundunar ‘Operation Forest Sanity’ ta Sojin Kasa na Najeriya sun ceto wasu mutum tara da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a Jihar Kaduna.
Dakarun sun samu nasarar kubutar da mutanen ne yayin wani samame da suka maboyar ‘yan bindigar da ke garin Kaso a Karamar Hukumar Chikun ta jihar.
- Ban ga laifin masu barin Najeriya don neman ingantacciyar rayuwa ba – Kakakin Buhari
- Qatar 2022: Zafin cin kwallon Moroko ya haddasa tarzoma a Belgium
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya ce sojojin sun yi artabu da ‘yan bindigar ne a babban titin Tantatu, lamarin da ya sa suka tsere cikin dajin.
A sanarwar da ya fitar a ranar Litinin, Aruwan ya ce Sojojin sun yi bincike a sansanin tare da ceto mutum tara da suka yi garkuwa da su.
“Sojojin sun kuma kwato shanu 90 da ‘yan bindigar da suka gudu suka bari wadanda za a mika su ga Hukumar Kula da Kiwon Dabobbi ta Jihar Kaduna domin tantance su,” in ji shi.
Ya ce an gudanar da wani samamen sirri a tsaunin Bawa Rikasa, inda aka samu nasarar kwato babura hudu a hannun barayin daji.
Aruwan, ya ce mutum tara da aka ceto za a tantance su kafin a sake sada su da iyalansu.