Dakarun Runduna ta Daya ta Sojin Kasa ta Najeriya sun ceto mutane tara da aka sace tare da kwato makamai a Karamar Hukumar Igabi ta Jihar Kaduna.
Mukaddashin Daraktan Hulda da Jama’a na rundunar, Laftana-Kanar Musa Yahaya, ya ce sojojin suna sintiri a yankin Kanzaure ne suka samu rahoton garkuwa da wasu mutane 11 a kauyukan Anguwan Maharba da Dandami.
- Mutum 16 sun mutu 27 sun jikkata a hatsarin tirela a Kaduna
- Abin da Dahiru Bauchi ya ce kan sauya sunan kauyen Tudun Biri
Yahaya ya ce sojojin sun yi wa ’yan bindigar kwanton bauna a mashigarsu, inda suka yi dauki ba dadi, suka kubutar da mutanen a ranar 8 ga watan Disamba, 2023.
“’Yan bindigar sun tsere bayan barin wutar inda sojojin suka ceto mutane tara, amma ’yan bindigar sun kashe biyu daga cikin wadanda suka sacen kafin isowar sojojin.”
A cewarsa, an samu kwato bindiga kirar AK47 guda daya da kuma bindiga kirar gida daya daga hannun ’yan bindigar.
Yahaya ya ce babban hafsan rundunar kuma kwamandan runduna Operation Whirl Punch, Manjo-Janar Valentine Okoro, ya yaba wa sojojin sannan ya umarce su da kada su yi kasa a gwiwa wajen tabbatar da tsaron ’yan kasa a yankin.
Okoro ya bukaci jama’a da su rika bai wa sojoji da sauran jami’an tsaro sahihan bayanan sirri don magance matsalar rashin tsaro a yankin.