✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun ceto mutum 7 daga hannun Boko Haram a Konduga

Mutanen da aka ceto dukkansu Fulani makiyaya ne da ta’addan sun yi wa garkuwa da su.

Dakarun sojojin Najeriya sun ceto wasu mutane bakwai da mayakan Boko Haram suka yi garkuwa da su a garin Kanama da ke Karamar Hukumar Damboa ta Jihar Borno.

Kwarraren masani mai sharhi kan masu tayar da kayar baya a yankin Tafkin Chadi, Zagazola Makama, ya ce sojojin sun ceto mutanen ne yayin wani samame da suka a ranar 18 ga watan Yulin 2024.

Majiyar Zagazola ta ce dakarun barikin soja na 25 da ke Damboa sun samu nasarar ce bayan tatsar bayanan sirri kan ayyukan ’yan ta’addan a garin Imimi da Bulabulin da ke karamar hukumar ta Konduga.

Majiyar ta ce, “sojojin sun gano wani katafaren sansanin ’yan Boko Haram a Imimi Bulabulin, inda ta yi galaba a kan ‘yan ta’addan ta hanyar kashe  daya daga cikinsu yayin da ragowar suka tsere.

“Sojojin sun kuma lalata wasu sansanoninsu, yayin da suka kwato wasu  kayayyakin da suka hada da kekuna 11, da akwatuna biyu na alburusan bindigar AK 47 da sauran kayayyaki daban-daban.

“A yayin haka ne kuma tawagar sojojin ta ci karo da wasu mutane bakwai da aka garkame su a cikin sarka a wajen wani sansanin ’yan tawaye a kauyen Kanama.

Bayanai sun ceto mutanen da aka ceto dukkansu Fulani makiyaya ne wadanda suka yi ikirarin cewa ’yan ta’addan sun yi musu fashi da garkuwa da su a lokuta da wurare daban-daban.

Aminiya ta ruwaito cewa wannan farmakin wani bangare ne na aikin rundunar “Operation Hadin Kai” na “Operation Desert Sanity III” da ke ci gaba da kawo karshen ayyukan ta’addanci a yankin.

Fulani makiyaya da sojojin suka ceto