✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun ceto mutane 4 da aka sace a Taraba

Wadanda aka ceto sun hada da dan Sarkin Kwaji, wanda aka sace tare da mahaifansa watanni uku da suka wuce

Sojoji daga Birget na 6 na Sojin Kasan Najeriya sun ceto wasu mutane hudu da ’yan bindiga suka sace a Karamar Hukumar Yorro ta Jihar Taraba.

Wadanda aka ceto sun hada da dan Sarkin Kwaji, wanda aka sace tare da mahaifansa watanni uku da suka wuce amma aka saki iyayen nasa.

Kakakin rundunar sojin, Laftanar Oni Olubodunde ya ce sojojin tare da hadin gwiwar wasu jami’an tsaro sun ceto mutanen hudu ne bayan musayar wuta da ’yan bindigan da ke kan wani tsauni, inda suke tsare mutanen da suke garkuwa da su.

Ya ce sojojin sun kona maboyar ’yan bindigan, lamarin da ya tilastawa ’yan bindigan tserewa.

Lautanar Oni Olubodunde ya ce a lokacin musayar wutan wasu daga cikin mutanen da ’yan ta’addan ke tsare da su sun samu damar tserewa daga inda ake tsare da su.

Ya ce jami’an tsaron na ci gaba da neman wadanda suka tsere domin a mayar da su ga iyalansu.

Jami’in ya bayar da tabbacin cewa za su cigaba da yaki da ’yan ta’addan da suka addabi al’ummar Jihar Taraba.

Lautanar Oni ya nemi jama’a da su rika bai wa sojoji da sauran jami’an tsaro labari a duk lokacin da suka ga wasu mutane wadanda ba su yarda da su ba da yankunansu.