✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sojoji sun ceto Matan Chibok 3 da ’ya’yansu

Ruwan wuta ya sa masu tayar da kayar bayan suke mika wuya.

Rundunar Sojin Najeriya ta ceto wasu mata uku daga cikin daliban Sakandiren Chibok da mayakan Boko Haram suka sace tsawon shekaru.

Rundunar Sojin karkashin rundunar Hadin Kai ce ta ceto matan uku da ’ya’yansu a Jihar Borno.

Shugaban rundunar, Manjo Janar Wahid Shu’aibu ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a shalkwatar rundunar da ke barikin Maimalari a Maiduguri a ranar Juma’a.

“Matan da sojojinmu suka ceto su ne Falmata Lawal, wacce aka kubutar a ranar 30 ga watan Agusta, da Asabe Ali, wacce aka ceto a ranar 1 ga watan Satumba, da kuma Jimkar Yarma wacce aka ceto a ranar 2 ga watan Satumba.

“Dukkaninsu daliban makarantar Chibok ne da aka sace.

“Sojojin sun ceto su ne tare ’ya’yansu wadanda suka haifa lokacin suna tsare a hannun ’yan ta’adda.

Manjo Janar Shuaibu ya ce wannan nasara na zuwa ne a sakamakon yadda suke ci gaba da yi wa maboyar ’yan ta’adda a musamman a Dajin Sambisa.

“Ruwan wuta da muke yi wa masu tayar da kayar bayan ya sa suke mika wuya, kuma a dalilin haka matan suke kubuta daga hannunsu.”