✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun ceto Kwamishinar Mata da aka sace a Kuros Riba 

Sojojin sun ceto Kwamishiniyar bayan shafe tsawon lokaci da sacewa.

Dakarun sojoji sun ceto Kwamishinar Harkokin Mata ta Jihar Kuros Riba, Misis Gertrude Njar daga hannun masu garkuwa da mutane.

Jami’in Hulda da Jama’a na Birged na 13 na Rundunar Sojin Najeriya da ke Kalaba, Kyaftin Dorcas Aluko, ta sanar a ranar Laraba, cewa kwamishinar da aka ceto tana samun kulawar likita, daga nan kuma za a sallame ta.

Ta bayyana cewa, “Sojojin sun yi wa masu garkuwa da mutanen kwanton bauna a kusa da Peter Effiong Creek.

“Dakarun soji da dabara sun yi kwanton bauna inda suka musu barin wuta, wanda hakan ya sa masu laifin guduwa su bar Kwamishinar da suka sace.”

Ta kara da cewa sojojin sun bi sahun ’yan bindigar domin kamo su, su gurfanar da su.

An yi garkuwa da Kwamishinar ce a ranar 1 ga watan Fabrairu a unguwar Mayne Avenue, a Kalaba ta Kudu.

Kyaftin Dorcas ta ce “Kwamandan Biriged na 13ya yaba wa sojojin da suka ceto ta, sannan ya bukaci su ci gaba da fatattakar duk wani mai aikata laifi a yankin.

“An kuma karfafa wa jama’a gwiwa da su ci gaba da bayar da sahihan bayanai kan aikata laifuka a yankunansu,” in ji ta.