Sojojin Najeriya sun ceto karin dalibai biyu da kungiyar Boko Haram ta yi garkuwa da su shekara takwas da suka gabata a Makarantar Sakandaren Kwana ta ’Yan Mata da ke Chibok a Jihar Borno.
Da yake gabatar da daliban da aka ceto bayan sun shekara takwas a hannun ’yan Boko Haram, Babban Kwamandan Rundun ta 7 da ke Maiduguri, Manjo-Janar Shuaibu Waidi, ya ce za a mika su ga Gwamnatin jihar Borno.
- Ambaliya: Najeriya na iya haduwa da tsananin yunwa a badi
- Shin kwayar magani ta P-Aladin na jawo ciwon koda?
Manjo Janar Shuaibu ya ce, Yana Pogu mai lamba 19 a jerin ’Yan Matan Chibok da aka sace, sojoji sun ceto ta ne tun a ranar 29 ga watan Satumba tare da yara hudu, a kauyen Mairari, a Karamar Hukumar Bama, a yayin wani sintiri na share fage.
“Hakazalika, a ranar 2 ga Oktoba, aka kara ceto Rejoice Sanki, wacce ke lamba 70 a jerin ’Yan Matan Chibok, sojoji sun ceto ta tare da ’ya’yanta biyu a yankin Kawuri,” in ji Janar Waidi.
Ya ce yanzu haka ana duba lafiyar daliban da aka ceto tare da ’ya’yansu domin a mika su ga gwamnatin Borno.
“A halin yanzu za sojojinmu sun ceto ’Yan Matan Chibok 13 a cikin watanni biyar da suka gabata.
“Ya zuwa yanzu, daga cikin ’Yan Matan Chibok 276 da ’yan ta’addan suka sace a shekarar 2014, saura 96 a hannun ’yan ta’addan Boko Haram.
Sabon sansanin tubabbun ’yan Boko Haram
Kwamandan rundunar hadin gwiwa ta Operation Hadin Kai (OPHK) da ke Arewa maso Gabas, Manjo-Janar Christopher Musa, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Maiduguri.
Manjo-Janar Christopher Musa ya kuma sanar da bude sabon sansanin karbar tubabbun ’yan Boko Haram da ke mika wuya, tare da ba da tabbacin cewa sabon sansanin na cikin wani wuri mai tsaro da sojoji za su iya tsare shi.
“Bisa kimantawa, mun duba wuraren da za a iya kare su yadda ya kamata,” in ji shi.