✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sojoji sun cafke shugaban kungiyar IPOB

An kama mataimakin kwamandan IPOB ya shiga hannu bayan an bindige maigidansa.

Sojojin Najeriya sun damke wani shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB ta ’yan-awaren kabilar Ibo.

An cafke Awurum Eze, wanda shi ne mataimakin shugaban bangaren tsaron IPOB ne kwanaki kandan bayan sojoji sun bindige maigidansa Ikonso, a Jihar Imo.

Kakakin Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya, Birgediya Mohammed Yerima, ya ce “Awurum Eze na daga cikin masu daukar nauyi kashe-kashe a Jihar Imo kuma jami’an tsaro sun kusa wata uku suna neman sa.

“Yawancin ’yan IPOB/ESN da aka kama sun ce yana cikin masu daukar nauyinsu da kitsa hare-haren, kuma shi ne mataimakin Ikonso.

“Sun shaida mana cewa Ikonso da Awurum da wasu shugabanninsu a Jihar Imo na da alaka kai tsaye da Nnamdi Kanu.

“Akwai hotuna da dama da suka dauka tare da Nnamdi Kanu. Hadin gwiwar jami’an tsaro zai ci gaba a kan lamarin.”

Yerima ya ce dubun Eze ta cika ne bayan ya tsere a lokacin samamen aka kai, wanda a cikinsa aka kashe Ikonso.

Ye ce Rundunar ta dade tana hakon mai shekara 48 din dan asalin Umoneke Nta, Karamar Hukumar Isiala-Mbano a Jihar Imo, kafin ta kama shi ranar Laraba a Jihar Abiya.