Sojojin Najeriya sun damke wani shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB ta ’yan-awaren kabilar Ibo.
An cafke Awurum Eze, wanda shi ne mataimakin shugaban bangaren tsaron IPOB ne kwanaki kandan bayan sojoji sun bindige maigidansa Ikonso, a Jihar Imo.
- Dalilinmu na Sallar Idi ran Laraba —Dahiru Bauchi
- Ndume ya soki Gwamnonin Kudu kan hana yawon kiwo
- Gadar Gwamna ta karye mako daya da kammalawa
Kakakin Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya, Birgediya Mohammed Yerima, ya ce “Awurum Eze na daga cikin masu daukar nauyi kashe-kashe a Jihar Imo kuma jami’an tsaro sun kusa wata uku suna neman sa.
“Yawancin ’yan IPOB/ESN da aka kama sun ce yana cikin masu daukar nauyinsu da kitsa hare-haren, kuma shi ne mataimakin Ikonso.
“Akwai hotuna da dama da suka dauka tare da Nnamdi Kanu. Hadin gwiwar jami’an tsaro zai ci gaba a kan lamarin.”
Yerima ya ce dubun Eze ta cika ne bayan ya tsere a lokacin samamen aka kai, wanda a cikinsa aka kashe Ikonso.
Ye ce Rundunar ta dade tana hakon mai shekara 48 din dan asalin Umoneke Nta, Karamar Hukumar Isiala-Mbano a Jihar Imo, kafin ta kama shi ranar Laraba a Jihar Abiya.