✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sojoji sun bude wa dalibai wuta a Jos

Dalibai sun yi zanga-zanga kan dage jarabawarsu da aka yi

Sojoji sun bude wuta a kan dalibai da ke zanga-zanga kan dage jarawarsu da aka yi a Kwalejin Kimiyya da Kere-kere ta Jihar Filato.

Harbe-harben sun jikkata dalibai da dama a kofar shiga harabar kwalejin da ke kan titin Yabubu Gowon a garin Jos a safiyar Litinin.

Daliban da suka tare hanyar sun kowa cewa sun shafe daren Litinin  suna karatu, bata tare da an sanar da su dage jarabawar ba, sai washegari da za a shiga jarrabawa da safe.

Sun kuma koka da cewa yajin aiki da rufe makarantar da aka yi a lokuta daban-daban sun tsawaita musu shekarunsu a makarantar, wadanda ke karatun kwasa-kwasan wata 18 sun shafe sama da shekara uku ba su kammala ba.

Ana cikin haka ne jami’an tsaro suka iso wurin suka bude wuta tare da harba hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa daliban daga wurin da ma harabar makarantar.

A garin haka ne wasu daga cikin daliban suka samu raunin harbi, wasu masu ciwon asma kuma suka shake da hayakin.

Wakilinmu ya ziyarci asibitin da aka kai daliban inda ya isa wani dalibi mai suna Azi Nyam Waziri da raunin harbi a gefen cikinsa, sai kuma Usendok Samuel Godwin wanda harbi ya same shi a goshi.

Waziri ya shaida masa cewa ba a cire harsashin da ya same shi ba, Godwin kuma ya ce bai sani ba ko harsashin na cikin kansa ko wucewa ya yi, saboda bai san inda kansa yake ba a lokacin da aka kawo shi asibitin.

Wakilinmu ya nemi zantawa da shugabannin kungiyar daliban kwalejin, amma bai same su ba, domin a lokacin suna ganawa da jami’an gwamanti a kan lamarin a gidan gwamnatin jihar.

A nashi bangaren, kakakin rundunar tsaro ta Operation Safe Haven, Manjo Major Ishaku Takwa, ya ce sojoji ba su yi harbi ba a wurin, zuwa suka yi don su kawar da shingen da daliban suka kafa a kan titi.

“Sanin kowa ne cewa ba a dade da yin wani rikici ba a Jos, saboda haka duk mai son yin zanga-zanga wajibi ne ya samu amincewar gwamnati, amma ba su yi ba, suka kuma tare babbar hanya, wanda hakan ya jefa masu bin hanyar cikin zullumi,” inji shi.

Dickson S. Adama da Ado Abubakar Musa, Jos da Sagir Kano Saleh