✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sojoji na samun nasara a yaki da Boko Haram —Zulum

Gwamnan ya ce, “Ya kamata mu ci gaba da ba su kwarin gwiwar don tabbatar da zaman lafiya mai dorewa.”

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya bayyana cewa sojoji na ci gaba da samun nasara a kan mayakan Boko Haram.

Hakan na dauke ne cikin wani jawabi da mai magana da yawun gwamnan, Isa Gusau  ya gabatar a wani taro tare da Hafsoshin Tsaro da ya gudana a ranar Lahadi.

A cewar Gwamnan, a baya-bayan nan sojoji sun samu nasarar kwato makamai daga hannun masu tayar da kayar bayan a garin Gwoza.

“Wannan ya nuna karsashi da jajircewar sojoji wajen samar da zaman lafiya, wanda ya kamata mu ci gaba da ba su kwarin gwiwar don samar da zaman lafiya mai dorewa,” a cewarsa.

Kazalika, Bataliya mai lamba ta 3 ta rundunar Operation Lafiya Dole, ta samu galaba a kan mayakan Boko Haram ranar Juma’a a kauyen Jigalta da ke kan hanyar Monguno zuwa Gajiram.

Aminiya ta samu rahoton cewa sojojin Bataliya ta 112 a garin Mafa, sun kwato wata babbar mota cike da makamai da babura daga ’yan ta’addar a kan hanyar Monguno zuwa Gajiram.