✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sojoji mata 200 za su yi sintiri a hanyar Abuja-Kaduna

An aike da sojojin mata don yakar ayyukan 'yan bindiga da suka addabi hanyar.

Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta aike da dakarunta mata 200 domin tsaron babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna, wadda ’yan bindiga suka addaba a tsawon lokaci.

Sojojin mata za su hade da rundunar ‘Operation Thunder Strike’ da ke  aikin samar da tsaro a kan hanyar ta Abuja-Kaduna.

Aminiya ta gano cewa wannan shi ne karo na farko da aka girke sojoji 200 kan hanyar, wanda yanzu adadinsu ya kai 300 idan aka hade da na baya da aka girke a hanyar.

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, yayin ganawa da sojojin mata a kauyen Kakau na jihar, ya ce matakin zai kawo zaman lafiya a hanyar.

Babban titin Abuja-Kaduna, ya dade cikin mawuyacin hali saboda irin yadda ’yan bindiga suka addabi matafiya.

Mutane da dama sun rasa rayukansu a hanyar, wasu an yi garkuwa da su sai da aka biya kudin fansa kafin ’yan bindiga suka sako su.