Wani ayarin sojojin kasa na Najeriya da jami’an hukumar tsaro ta DSS sun sami nasarar dakile yunkurin wasu ’yan ta’adda na kai hari Karamar Hukumar Gazawa da ke Jihar Kano.
Kakakin Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya, Birgediya Janar Onyeama Nwachukwu, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwar da ya wallafa a shafin rundunar na X (Twitter a da) ranar Juma’a.
Ya ce sun kai samamen ne da nufin kama wasu da ake zargin ’yan Boko Haram ne da ke kokarin kai wani kazamin hari a Kano.
Ya ce, “A wani samame da muka kai maboyar ’yan ta’addan da sanyin safiyar Juma’a, 3 ga watan Nuwamban 2023, dakarun runduna ga 3 ta sojin kasa na Najeriya tare da hadin gwiwar jami’an DSS, sun kai wani shiryayyen samame a Karamar Hukumar Gezawa ta Jihar Kano.
“A sakamakon haka, dakarun sun sami nasarar kama wadanda ake zargin ’yan Boko Haram ne su biyu, wadanda yanzu haka suke hannunmu.
“A yayin samamen, dakarun sun kwato bindigogin AK-47 guda biyar, manyan bindigun AK-47 masu sarrafa kansu guda biyar, na’urar harbo jiragen sama guda daya, bama-bamai guda biyar, gurneti guda 10, kakin sojoji guda biyar sai jakunkunan saka bindigogi guda 10 da kuma wasu sinadaran hada bama-bamai.
“Hadin gwiwa da aiki taren da ake samu tsakanin sojoji da sauran jami’an tsaro da aka gani yayin wannan aikin ya nuna karara yadda dukkanmu muke kokarin hada kai don ganin bayan ta’addanci da ma duk wani kalubalen tsaro.
“Hakan kuma ya dada tabbatar fafutukar da sojojin Najeriya ke yi wajen kare rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya,” in ji Kakakin sojojin.