✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojin Larabawa sun kakkabo jiragen ’yan Houthi a Saudiyya

Sun tarwatsa jiragen mayakan Houthi makare da ababen fashewa a Bahar Maliya.

Rundunar kawancen kasashen Larabawa da Saudiyya ke jagoranta sun baro jiragen yaki marasa matuka na ’yan tawayen Houthi na kasar Yemen.

Rundunar ta kama jiragen ne makare da ababen fashewa a yankin Kudancin Saudiyya ta kuma ta tarwatsa su.

Kakakin Rundunar, Kanar Turki Al-Maliki ya ce: “A safiyar Alhamis rundunar ta cafke jirage mara matuki dauke da makamai da ’yan tawayen Houthi suka kai wa fararen hula hari da su a yankin Kudanci”.

Harin na zuwa ne bayan a ranar Laraba sojin ruwan rundunar kawancen sun tarwatsa wasu jiragen ruwan mayakan Houthi makare da ababen fashewa a kan tekun Bahar Maliya.

A baya-bayan nan ’yan tawayen na Yemen sun tsananta kai hare-hare a makwabtan kasar sabanin dokokin kasashen duniya da ma na cikin gidan Yemen din.