Rundunar kawancen kasashen Larabawa da Saudiyya ke jagoranta sun baro jiragen yaki marasa matuka na ’yan tawayen Houthi na kasar Yemen.
Rundunar ta kama jiragen ne makare da ababen fashewa a yankin Kudancin Saudiyya ta kuma ta tarwatsa su.
- Bam ya tashi a wata makabarta a Saudiyya
- Firaministan Bahrain ya rasu bayan shafe shekaru 49 a kan mulki
Kakakin Rundunar, Kanar Turki Al-Maliki ya ce: “A safiyar Alhamis rundunar ta cafke jirage mara matuki dauke da makamai da ’yan tawayen Houthi suka kai wa fararen hula hari da su a yankin Kudanci”.
Harin na zuwa ne bayan a ranar Laraba sojin ruwan rundunar kawancen sun tarwatsa wasu jiragen ruwan mayakan Houthi makare da ababen fashewa a kan tekun Bahar Maliya.
A baya-bayan nan ’yan tawayen na Yemen sun tsananta kai hare-hare a makwabtan kasar sabanin dokokin kasashen duniya da ma na cikin gidan Yemen din.