Sojojin Isra’ila sun kai hari Kudancin Lebanon da zirin Gaza a daidai lokacin da Firaministan Isra’ila ke cewa abokan gabarsu za su dandana kudarsu bayan da ya zargi mayakan Hamas da kai hare-haren rokoki kan Isra’ila.
Dakarun sojin Isra’ila sun kai harin ne wasu wurare a Lebanon da Gaza da sanyin safiyar Juma’a.
Harin dai na zuwa ne a matsayin ramuwar gayya kan hare-haren rokoki da suka dora alhakinsa kan kungiyar Hamas, daidai lokacin da ake ta kai ruwa rana kan farmakin da ‘yan sandan Isra’ila suka kai cikin masallacin Al-Aqsa da ke birnin Kudus a makon nan.
Fashe-fashe masu karfi sun girgiza yankuna daban-daban na Gaza, a daidai lokacin da Isra’ila ta ce jiragenta sun kai farmaki kan wasu wurare da suka hada da na kera makamai na Hamas da kuma wasu hanyoyin da aka haka a karkashin kasa.
Rundunar sojin kasar ta ce ta kuma kai hari kan mayakan Hamas da ke kudancin kasar Lebanon, inda mazauna yankin da ke kusa da sansanin ‘yan gudun hijira na Rashidiyeh suka sanar da tashin bama-bamai uku.
Harin dai ya zo ne a matsayin martani kan hare-haren rokoki da aka harba daga Lebanon zuwa yankunan Arewacin Isra’ila, wanda jami’an Isra’ila suka dora alhakinsa kan Hamas.
Rundunar sojin ta ce an harba rokoki 34 daga kasar Lebanon, inda suka yi nasarar tare 25 daga cikinsu.
Wannan dai shi ne hari mafi girma da aka kai tun daga shekarar 2006, lokacin da Isra’ila ta gwabza yaki da kungiyar Hizbullah da ke dauke da muggan makamai.