✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojantar da Hukumar NIMASA

Hukumar Kula da Harkokin Tsaron Tashoshin Jiragen Ruwa ta Najeriya (NIMASA) ta rika samun kanta a cikin cece-kuce tun lokacin da Shugaba Goodluck Jonathan ya…

Hukumar Kula da Harkokin Tsaron Tashoshin Jiragen Ruwa ta Najeriya (NIMASA) ta rika samun kanta a cikin cece-kuce tun lokacin da Shugaba Goodluck Jonathan ya nada Mista Ziakede Patrick Akpobolokemi a matsayin Darakta Janar na hukumar da kuma Mista Gobernment Ekpemupolo, da ake wa lakabi da Tompolo, wani tsohon dan ta’addan Neja-Delta a matsayin shugaban kwamitin amintattunta.
A karkashin dokar NIMASA ta shekarar 2007, Mista Akpobolokemi bai cancanci wannan mukami ba, saboda karancin shekarunsa. Kuma tun lokacin ake fama da matsalar fitar da kudade daga asusun NIMASA ba tare da samun amincewar hukumar gudanarwar ba.
Kuma ana yawan samun rikici a tsakanin hukumar da wasu kamfanonin kasuwanci kamar Kamfanin Iskar Gas na Najeriya (NLNG) kan biyan kudin haraji, abin da ya jawo gagarumar asara wajen fitar da kaya ga kamfanin.
Takaddamar da ta shafi bayar da kwangilar biliyoyin Dala sabunta kwantaragin kula da tashoshin jiragen ruwa da bututun mai ga wani kamfani mallakar Tompolo har yanzu gwamnati ta gaza warware ta yadda ya kamata.
A baya-bayan nan kuma sai ga rahotanni a kafafen watsa labarai na kasar Norway cewa Tompolo ya sayo wasu jiragen ruwan yaki daga Norway da ba a kaddamar da su ba, kuma har a cewar rahotannin jiragen sun hada da jiragen yaki masu dauke da makamai samfurin Hauk-class guda shida da suke dauke da rokoki.
Lura da tarihin Tompolo da irin halayen da yake nuna a baya-bayan nan, wadanda suka hada da soke wani taro a Jihar Delta da aka sa ran Shugaba Jonathan ya zama babban bako, abin na baya-bayan nan in aka hada da na baya suna iya kawo damuwa.
daya daga cikin wakilan Majalisar Tarayya ya kira sayo jiragen yaki da “abin tsoro,” duk da kokarin da Darakta Janar na NIMASA, Akpoolokemi ya yi na share batun.
Akalla Akpobolokemi ya yi ikirarin cewa jiragen na yaki ne, amma ya ce an sayo ne wa sojojin ruwa wadanda ya ce suna amfani da su domin ‘tsaron’ iyakokin ruwa na Najeriya.
“Sojojin ruwa ne suka sanya bindigoginsu a kan jiragen ruwa don taimaka musu wajen tsaron iyakokin ruwa. Hukumar NIMASA dai ta kunshi fararen hula wadanda kwararru ne a fannoni da dama da ba su da wata jam’iyyar siyasa ko wata bukata ta kashin kai. Kuma a matsayinta na wani bangare na gwamnati da ke kula da tsaron tashoshin jiragen ruwa da karewa da tsara dokoki da sauransu, muna aiki da sojojin ruwa da sauran hukumomin tsaro don yin amfani da jami’ai da makamansu wajen sintiri da bayar da tsaro ga hanyoyin ruwan kasar nan,” inji shi.
Ba abin mamak ba ne da Akpobolokemi ya gaza nuna cewa ayyukan NIMASA bai shafi amfani da makamai ko sayo kayan yaki ba. Kuma NIMASA ta yi ruwa da tsaki kan muhawara game da bukatar a kirkiro Hukumar Tsaron Tashoshin Jiragen Ruwa (Maritime Security Agency – MASECA) domin cimma nasara Kwamitin Shugaban kasa kan Tsaro da Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa (PICOMSS).
Manufar hakan a bayar da kariya ga jiragen ruwa na ’yan kasuwa sakamakon ayyukan mafasan cikin teku. Sai dai Majalisar dinkin Duniya ta nuna damuwa kan cewa MASECA na iya cin karo da dokokin kasashen duniya kan tsaro da kula da lafiya a cikin teku, wadanda ba su yarda jiragen ’yan kasuwa su rika amfani da makamai ba.
Don haka akwai tufka da warwara a nan, yaya za a yi sojojin ruwan Najeriya su dogara da sayo makamai da sauran kayan yaki daga wani mutum daya, idan akwai matsala wajen gudanar da aikinsu na kare iyakokin ruwan kasar nan? Alakar da ke tsakanin jami’an sojan ruwa da kamfanin da ke da hannu a sayo jiragen yaki na bukatar a bayyana ta a karkashin wani kwamitin bincike na musamman.
Na biyu sintiri a cikin ruwa don a hana mafasan cikin teku, ba ya bukatar sayo samfurin jiragen yaki na Hauk-class da jirage masu dauke da rokoki. Domin wadannan manyan jiragen ba za su iya fuskanta su samu nasarar hana mafasan ba, wadanda galibi da kananan jiragen ruwa masu gudu suke amfani, wadanda za su iya bace wa Hauk-class cikin kankanen lokaci. Hakika fashi a cikin teku yana karuwa a ’yan shekarun nan, sakamakon yadda barayin danyen mai suke karuwa duk da kwantaragin masu sanya ido da ke akwai.
A fili yake cewa dukkan bayanan da dan kwangilar Tompolo da abokin ciniki NIMASA bas u gamsar ba. Ya kamata a samar da dalili mai kwari na sayo jiragen yakin da kamfanin da tsohon dan ta’addan yake gudanarwa. Kuma ta hanyar bincike daga Majalisar Dokoki ta kasa ne kawai za a iya gano alakar da ke cikin haka kuma a sanya aya ga karuwar mayar da tashoshin jiragen ruwan Najeriya wani sansani na soja.