Wani jami’in sojan Najeriya ya kashe kansa bayan da ya harbe wani jami’in kwastam da suke aiki tare a Legas.
A daren ranar Laraba 02/06/2021 Kofur Mahmud Sulaiman, daga Bataliya ta 243 ta Sojin Najeriya ya bude wa Isfekta CN. Walter wuta a babban shingen jami’an tsaro da ke yankin Oloko a Gbaji a kan hanyar iyakar Najeriya da kasar Jamhuriyar Benin a Shiyyar Seme, lamarin da ya tayar da hankalin al’ummar yankin.
Kakakin Hukumar Kwastam a shiyyar Seme, Abdullahi Hussain ya ce “Yanzu haka ana gudanar da bincike domin sanin musababbin lamarin,” kuma sojan ya kashe kansa ne bayan da ya harbe jami’in kwastam din.
Wani mazaunin iyakar ta Seme da bai so a fadi sunansa ba ya shaida wa Aminiya cewa shingen jami’an tsaro na Gbaji da lamarin ya faru shi ne shinge mafi girma a kan iyakar Najeriya da Jamhuriyar Benin.
Bayanai sun nuna cewa sojan da ya yi kisan an yi masa sauyin wurin aiki ne daga Rundunar Operation Lafiya Dole mai yaki da kungiyar Boko Haram.
Wakilin Aminiya ya ziyarci yankin Seme, inda ya ga tarin manyan jami’an sojin kasa da kwastam da sauran hukumomin tsaro na yin sintiri bayan kashe jami’in kwastam din da sojan ya yi.