✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Soja ya kashe matuƙin Keke NAPEP a Jos

Sojan ya zaro wuƙarsa ya daɓa wa marigayin a ƙirji. Bayan an kai shi asibitin da ke barikin aka tabbatar da rasuwarsa.

Wani sojan da ke aiki da shiyya ta 3 ta Rundunar sojojin Najeriya a barikin Rukuba da ke Jos a Jihar Filato, ya daɓa wa wani matuƙin babur mai ƙafa uku (Keke NAPEP) mai suna Abdullahi Muhammad, wanda kuma makiyayi ne har lahira.

Shugaban Ƙungiyar Ci gaban Fulani ta Gan Allah (GAFDAN), Garba Abdullahi, ya shaida wa manema labarai a Jos cewa sojan ya kashe Muhammad mai shekara 26, a Gebu-Bassa, kusa da babbar ƙofar shiga barikin.

Ya yi Allah wadai da kisan gillar tare da yin kira ga shugabannin rundunar da su tabbatar da adalci ga mamacin.

Kakakin rundunar ta 3 LT Kanal Aliyu Danja ya tabbatar da faruwar lamarin.

A cewar shugaban Ƙungiyar ta GAFDAN, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7:00 na dare inda marigayin ya tsaya ya sayi wani abu kusa da ƙofar barikin.

Ya ce, “Bayan marigayin ya sayi abin da ya yi niyyar siya, sai ya shiga babur ɗin nasa mai ƙafa uku, yayin da ya juya baya, ya taka ƙafar sojan cikin kuskure. Da ya fahimci abin da ya faru, sai ya fito daga cikin keken, ya ba da haƙuri, amma duk da haka sai sojan da ke cikin farin kaya ya mare shi, sai hatsaniya ta kaure.

“Tun kafin nan, sojan ya zaro wuƙarsa ya daɓa wa marigayin a ƙirji. Bayan an kai shi asibitin da ke barikin aka tabbatar da rasuwarsa. Nan take abokan aikinsa suka kama sojan, inda da farko suka ɗauka farar hula ne amma daga baya suka gano shi soja ne,” in ji shugaban.

Mahaifin marigayin Alhaji Muhammad ya yi kira ga shugabannin sojojin Najeriya da su tabbatar da adalci ga yaronsa.

Da yake bayar da ƙarin bayani kan yadda aka kashe marigayin, kakakin runduna ta 3 ya ce, “Wannan abin baƙin ciki ya faru ne biyo bayan wata hatsaniya tsakanin marigayin da wani soja na ɗaya daga cikin bataliyoyinmu. Rahotannin farko na nuni da cewa lamarin ya yi ƙamari, wanda ya sa Abdullahi ya samu raunuka da wuƙa.