✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Soja ya kashe jami’in DSS saboda dan damfara

Tuni jami'an ’yan sanda suka fara gudanar da bincike.

Wani soja ya aika wani jami’in hukumar tsaro ta DSS lahira bayan takaddama ta barke a tsakaninsu kan kama wani dan damfara.

Kamfanin Dillacin Labarai na Najeriya (NAN), ya ce ana zargin sojan da kashe jami’in DSS din ne ta hanyar caka masa wuka a wuya, ranar Juma’a da dare.

  1. Ana kashe N211m wajen kwashe shara duk wata a Kaduna —Kwamishina
  2. An cafke mutum biyu da jabun kudi a Kwara
  3. ’Yan sanda sun kashe ’yan bindiga 4 a Imo

Lamarin ya faru ne bayan sojoji sun cafke wani da ake zargi dan damfara ne a wani otal da ke garin Ado-Ekiti, Jihar Ekiti.

Majiyar NAN ta ce, “Sojojin da ke otal din sun cafke wani matashi da suke zargin dan damfara ne, shi kuma da ya hangi jami’in DSS din sai ya nemi ya cece shi daga hannunsu.

“Bayan jami’in DSS ya tunkari sojojin sai musu mai karfi ya barke a tsakaninsu, a nan ne wani soja ya fusata ya zaro wuka ya caka masa a wuya.

“Nan take ya fadi cikin jini, mutane da ke cikin otal din kowa ya ce kafa me na ci ban baki ba,” a cewar majiyar.

Ta kara da cewa, ba jimawa da faruwar lamarin jami’an DSS suka bayyana a otal din tare da cafke sojojin.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ekiti ta ce ta fara bincike kan zargin kisan da aka yi wa jami’in.

ASP Sunday Abutu, wanda shi ne kakakin ’yan sandan jihar, ya ce ana zargin gardama tsakanin mamacin da wasu sojoji ne ya yi sanadiyyar mutuwarsa.

“Muna da labarin kashe jami’in DSS da aka yi a sakamakon musu da ya kaure tsakaninsa da wasu sojoji a yammacin ranar Juma’a.

“An kai gawar mamacin dakin ajiye gawa kuma ina tabbatar muku cewa nan ba da jimawa ba za a kamo wadanda suka kashe shi.

“Jami’anmu sun riga sun fara bincike kan lamarin don gano ummulhaba’isin mutuwar tasa,” a cewar Abutu, yayin tabbatar faruwar lamarin.

Kamfanin Dillacin Labarai na Najeriya (NAN), ya rawaito cewar lamarin ya faru a Ado-Ekiti, inda ake zargin wani soja ya kashe jami’in na DSS.