✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Soja ya karya wa nas kafa a kan kayan haihuwar matarsa

Nas din na kwance a asibiti ana jinyar ta, shi kuma sojoji sun kulle shi.

Wani soja ya lakada wa wata malamar jinya duka har ya karya mata kafa saboda ta bukaci kayan haihuwa daga matarsa da ya kai asibiti za ta haihu.

Lamarin ya faru ne bayan sojan da ke aiki a Barikin Sojoji na Sobi Cantonment da ke Ilorin a Jihar Kwara ya kai matarsa da ke cikin nakuda asibiti.

Dambarwar ta fara ne bayan nas din ta bukaci a kawo kayan haihuwar matar sojan, bayan an shigar da matar dakin haihuwa a karshen mako.

Majiyarmu ta ce, “Maimakon ya sayo kayan haihuwar, sai ya yi watsi da bukatar, bisa hujjar cewa gwamnatin jihar ta dauke wa masu juna biyu nauyin kayan haihuwa a asibiti.

“Nas din ta shaida masa cewa ba haka ba ne, mutane ne ba su fahimci bayanin gwmantin jihar ba, saboda haka ya kamata ya sako kayan domin a samu a karbi haihuwar matar tasa da su a dakin haihuwa”.

“Wannan ce fa maganar da ta fusata sojan, ya kama jibgar nas din har ya karya mata kafa daya”, inji wata majiyar ta daban.

Lamarin dai ya sa an kwantar da nas din a asibitin, inda a halin yanzu ake jinyar ta.

Wakilinmu ya tuntubi kakakin Birget na 22 na Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya da ke Barikin Sobi Cantonment, wanda ya tabbatar cewa wani soja na mai mukamin Staf Sajan, mai suna Wasiri ne ya yi aika-aikan.

Ya ce tuni aka kulle sojan domin gudanar da bincike a kansa, saboda danyen aikin da ya yi.