✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sirrin nasarar cinikin takalma a Ghana

Shirin African Dream na kafar yada labarai na BBC, wani shirin musamman ne da ke duba nasarorin da wasu ‘yan kasuwa daga nahiyar Afirka suka…

Shirin African Dream na kafar yada labarai na BBC, wani shirin musamman ne da ke duba nasarorin da wasu ‘yan kasuwa daga nahiyar Afirka suka samu. Kowannensu zai bayyana irin kalubalen da ya fuskanta da kuma yadda kasuwancinsa yake bunkasa. 

Duk da cewar bai da ilimin yadda ake hada takalma, Fred Deegbe wanda tsohon ma’aikacin banki ne, ya lashi takobin zama babba mai kera takalma a fadin duniya. Tun bayan da ya hadu da abokinsa suka kafa wani sabon kamfani, mai suna Heel The World (HTW), a shekara ta 2011 a birnin Accra lekafarsu take ta samun ci gaba. A yanzu kamfanin na da ma’aikata 13 domin kera takalma wadanda ake kai wa kasuwannin duniya.
Da aka tambaye shi: Ta yaya takalmanka ke goggaya da wadanda aka yi a kasar China?
Sai Mista Deegbe ya kada baki ya ce: “Kayayyakin kasar China ba abin damuwa ba ne gare ni. Saboda ina aiki ne da wasu tsare-tsare da ke taimakawa hajoji na: Hamayya na da dadi amma akwai wuya. A don haka ina tabbatar da cewar ina kera takalma da babu wanda ke da irinsu a kasuwa. Abu na biyu, muna bai wa inganci fifiko ba farashi ba. Na uku, ina mayar da hankali kan mutanen da ke son kayayyaki na musamman. Na hudu, ina tallata kayayyakina a inda babu su. Na biyar, takalman da nake kirayawa kirar hannu ne, ba na inji ba. Na shida, ina haba-haba da abokan hurda, saboda ta haka ne mutane ke sha’awar ci gaba da yi mani ciniki. Na bakwai, ina daukar matasa masu kwazo aiki domin fito da samfuri iri daban-daban. Na takwas, jagorantar yekuwar kayayyakin da aka kera a Ghana saboda mutane su san mahimmancin kayan gida. Na karshe kuma shi ne hangen nesa, ina yawaita tunanin yadda hajojina za su samu karbuwa tsakanin al’umma,” inji shi.