Ta faru ta kare, an yi wa mai dami daya sata, a gasar Zakarun Turai, 2023/2024 inda Real Madrid ta zama zakara kuma ta sake kafa tarihin lashe kofin a karo na 15 a tarihin gasar da aka faro a 1955/1956.
Shi kansa kocin kulob din Carlo Ancelotti, ya ce nasarar da suka samu, “ta wuce tunanin mutum,” an ruwaito shi yana fadin haka ne jim kadan bayan tashi daga wasan.
Abin lura a nan, shi ne yadda kulob din ya lashe kofin na UCL har sau shida a kaka 11 duk da yadda ya tsallake wasannin rukuni ba tare da kalubalen a zo a gani ba.
Sai dai za a iya cewa kulob din ya yi ta tsallake rijiya da baya a dukkan matakan kifa-daya-kwale, sakamakon yadda aka yi hasashen yiwuwar nasararsa bai wuce kashi 30 cikin 100 a wasannin ba.
Daga kakar 2014, Real Madrid, sau kalilan ne kawai ta shiga gasar a matsayin kungiyar da ke da karsashin tabuka abin kirki, lura da sau hudu kacal ta ci kofin La Liga. Tana bin bayan Barcelona – a galibin wadannan shekaru.
Abin da ke taimakon Madrid wajen samun nasara
A bangaren Toni Kroos ya ce da aka kai hutun rabin lokaci a wasan karshen ba tare da Dortmund ta jefa kwallo a raga ba, hakan ya sa Madrid yin amanna cewa za ta yi galaba a kan Dortmund idan aka dawo hutun rabin lokaci.
Da yake magana bayan kammala wasan, Kroos ya ce: “Babban abin da ya sa muka ci wasan shi ne ba mu bari sun jefa mana kwallo a raga gabanin tafiya hutun rabin lokaci ba.
“Wannan ya yi matukar taimaka mana. Mun dauki lokaci kafin mu ci karfin wasan.”
“Mukan lalubo hanyar samun nasara da maido da karsashinmu bayan an rinjaye mu a farkon wasa,” in ji Gareth Bale, tsohon dan wasan Real kamar yadda ya shaida wa jaridar The Guardian a farkon makon nan.
“Abin da ke tunzura mu ke nan; abokan hamayyarmu kan yi kokarin rinjayar bajin kulob din maimakon kungiyar.
“Akwai wani sirri tattare da haka, Real Madrid da Kofin Turai. Kungiyoyi na shakkar taka leda da Real Madrid wanda hakan ba karamin sirri ba ne,” in ji shi.
A tsokacin tsohon kocin kulob din, Jose Mourinho ya nasabta abin da tsari ko turbar da kulob din ke bi a matsayin abin da ke taimaka masa ya kere kowa a Turai.
Mourinho ya bayyana haka ne ga tashar TNT Sports a filin wasa na Wembley, bayan Madrid ta doke Borussia Dortmund da ci 2-0.
Ya ce: “Tsarin da Real Madrid shi ne kawai. Tana da Florentino Perez (shugabanta) da Jose Angel Sanchez, da babban mai farautar ’yan wasa da kuma koci. Shi ne kawai. Zancen gaskiya ke nan kuma shi ne dalilin nasararsu.”
Wani mai goyon bayan kulo din a Abuja, da ya ce sunansa SKD din Arewa ya ce daga cikin manyan abubuwan da mai horar da Kungiyar Real Madrid ya yarda da su kuma yake fada wa ’yan wasansa koyaushe kalamai uku ne da suke tsuma ’yan wasan.
Ya ce: “Shi kansa Ancelotti ya fayyace su a wata tattaunawa da ya yi da jaridar Marca.
“ Na farko koyaushe yana fara kawo wa ’yan wasansa muhimmanci farin cikin iyalansu, kamar yadda yake fada a ka’idar wasan dole ne sai ’yan uwan wasu sun yi farin ciki na wasu kuma su kwana cikin kunci.
“To su tabbatar iyalansu ne suka kwana cikin farin ciki.
“Abu na biyu kuma yana kara tunatar da su wasan karshe ya kunshi yin abu daya ne: Nasara. Idan har sun kasa sa kwallo a raga, to kada su bari a ci su.
“Ka ga idan har aka buga kunnen doki, karshe za a je bugun finareti, ka ga a nan dole sai daya ya yi nasara.
“Carlo Ancelotti koci ne da yake da tarihi a bangare iya ware ’yan wasa su iya bugun finareti, daga cikin irin wannan wasan da ya buga guda 18 ya ci guda 17 ɗaya kacal ya rasa.
“Abu na karshe kuma mafi muhimmanci shi ne, kada su zama masu zubar da damarmaki ta hanyar son kai, su tabbatar kwallo tana kafar wanda ya fi damar ci kafin su buga, saboda asarar damarmaki a wasa na kawo wa kungiya cikas musamman a wasan da yake da minti 90 kacal,” in ji shi.
Wani mai sharhin wasanni kuma magoyin bayan Real Madrid a Kaduna, mai suna Jossy ma ya alakanta nasarar kulob din da azamar da ’yan wasan suke sanyawa a ransu a duk lokacin da suke buga wasan Zakarun Turai.
“Sannan sun sanya wannan gasa a zukatansu cewa kowane kulob za su buga da shi, kawai za su samu nasara a kan kulob din.
“Koda ana cin su, suna da yakinin za su iya farkewa su yi nasara koda mintuna kadan suka rage a tashi. Gwiwarsu ba ta sanyi in dai a gasar Zakarun Turai ne.
“Kuma kowane kulob in dai yana wasa da Madrid a gasar suna buga wasan da shakkar cewa koda mun ci su za su rama. A ganina, wannan azamar ta taimake su kwarai da gaske.
“Sannan, ’yan wasan tsakiya sun yi matukar taimaka wa kulob din duk da Real ba ta da Lamba 9 na gaske amma a haka ta tabuka har ta ci kofin,’’ in ji shi.
Har wa yau, akwai masu ganin akwai himma da kwazon da ’yan wasan suke nunawa a tsakaninsu domin samun gurbi na farko a kulob din, shi ma ya taka muhimmiyar rawa wajen nasarar kulob din a kakar bana.
SKD din Arewa ya ce, “Akwai batun gogayya tsakanin ’yan wasan saboda kowane dan wasa yana ganin in bai tabuka abin a zo a gani ba; to kuwa dan uwansa in ya fi shi bajinta, zai sa ya rika zaman benci ke nan, musammam ma matasan ’yan wasan kulob din.”
Ya kara da cewa tasirin manyan ’yan wasan da suka ga jiya suka ga yau a kulob din irin su Toni Kroos da Luka Modric da Carvajal da kuma Kyaftin Nacho Fernandez da kowanensu ya ci kofin Zakarun Turai sau shida a tarihi ya yi matukar taimaka wa kungiyar wajen samun nasara sakamakon gogewarsu a buga wasannin karshe.
“Dadin dadawa kuma, shi kansa Shugaban kulob din, Florentino Perez ba karamin mai hangen nesa ba ne wajen sayo ’yan wasan da suke da gogewa kuma suke wasa da zuciyar lallai sun zo ne su taimaka wa kulob din.
“Dubi yadda ya kawo su Rudiger da Alaba da Vinicius da Valverde da Rodrygo da Joselu da Diaz da sauransu.
“Ga kuma yanzu ya kara kawo Kylian Mbappe da Endrick wanda dukkansu zakakuran ’yan wasan gaba ne,” in ji shi.
Shin akwai mai iya takawa Madrid birki a Turai kuwa lura da yadda ta kama hanyar dawo da tsohon tsarinta na hada ‘zakakuran ’yan kwallo na duniya’ da ake kira da ‘Galacticos?’ Lokaci ne zai zama alkali.