✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sirrin da ke cikin sana’ar jimar fata- Shu’aibu Inusa

Wani mai sana’ar jimar fata a Jihar Legas mai suna Shu’aibu Inusa ya ce sana’ar tana da sirri, ta kuma ishi duk mai yinta rayuwa…

Wani mai sana’ar jimar fata a Jihar Legas mai suna Shu’aibu Inusa ya ce sana’ar tana da sirri, ta kuma ishi duk mai yinta rayuwa cikin rufin asiri. 

Malam Shu’aibu dan shekara 30 dan asalin karamar Hukumar Madobi a Jihar Kano ya bayyana hakan ne a makon jiya a lokacin da yake tattaunawa da Aminiya.
Ya ce: “Mafi yawan mutane suna yi mana kallon wahala muke yi, ba ma samun komai a wannan sana’a, dalilin da ya sa suke ganin haka shi ne, don ba su san sirrin sana’ar ba. To amma mu da muka san sirrinta, mun san ba wahalar banza muke yi ba, domin muna samun rufin asiri.”
Ya ce gadon sana’ar ya yi, “Ita wannan sana’ar da kake gani ana samun alheri mai yawa a cikinta. Domin ni kaina tasowa na yi na tarar mahaifina yana yi shekara da shekaru, ba shi da sana’ar da ta fi jimar fata. Ni ma da ita nake daukar dawainiyar rayuwata da ta iyalina.”
Ya ce babu fatar da ba ya iya jemewa, kasancewar ya taso ya ga yadda mahaifinsa yake yi, a yanzu “babu fatar da ba na jemewa daga ta jimina da ta saniya da ta raguna da kuma ta awaki, kuma kudinsu ya danganta da girman fatar.”
Ya bayyana cewa yakan karbi Naira 1, 000 ko 3, 500 har zuwa 4, 000 ya danganta da girman fatar.
Ya kara da cewa mafi yawa malamai ne suka fi yin amfani da ita da kuma wasu daidaikun mutane masu sha’awa.
A cewarsa idan akwai akwai aiki sosai yakan samu Naira 5, 000 zuwa 7, 000.
Ya ce kayayyakin da yake amfani da su sun hada da ‘kusoshi’ da ‘wuka’ da ‘guduma’ da ‘katako’ da ‘dutse’ da kuma ‘butar ruwa’.