✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Sirrin Aiki’

Assalamu alaikum Manyan gobe tare da fat n ana lafiya? A yau na kawo muku labari ne akan ‘Sirrin Aiki’. Labarin ya yi nuni ga…

Assalamu alaikum Manyan gobe tare da fat n ana lafiya? A yau na kawo muku labari ne akan ‘Sirrin Aiki’. Labarin ya yi nuni ga abubuwan da yakamata mutum ya sani a lokacin aiki. A sha karatu lafiya.

Taku; Amina Abdullahi.

An yi wani sarki a wani kauye wanda yake son sanin irin halayyar mutanen kauyen sannan ya yi alkawarin bada kyauta mai tsoka ga duk wanda ya dace.

Ya kira Dogaransa ya sanya su su isar da wannan sako ga jama’arsa. Sai suka shiga kauyen suka tarar da wani kafinta yana kera kujera sai suka tambaye shi ko yana son wannan aikin da yake yi? Ya ce musa baya son wannan aiki kuma yana yin sa ne kawai saboda yana bukatar kudi.

Sai suka kara gaba suka tarar da wani mai wankin kaya a fusace koda suka tambaye shi ko yana son aikin da yake yi, sai ya amsa musu a fusace cewa ya kasance mara son zuwa makaranta a lokacin da yake karami shi ya sa yanzu babu yadda ya iya face ya yi sana’ar wanki.

Da yamma ta yi sai dogarai suka ce bari su koma a kan hanyarsu ta komawa ne sai suka hango wani daki daga nesa mai hasken fitila.. Suna isa sai suka ga wani malami da dalibai da yawa yana koya masu karatu. Suna tambayarsa ko yana son abin da yake yi ya ce kwarai kuwa.

Dogarai suka kai shi wajen Sarki. Sai ya dauki kyauta mai tsoka ya danka wa malamin. Sarki ya ce babu sirrin aiki da ya kai mutum ya kasance yana son abin da yake yi.

Tare da fatan manyan gobe za su sanya ido a karatu sosai domin zama mutane nagari a gaba.