✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sinadaran cikin abinci

A wasu lokuta kakan ambaci nau’ikan abinci iri-iri, kamar sinadaran bitaman da mineral. Me zai hana a yi mana bayani a kansu da irin aikin…

A wasu lokuta kakan ambaci nau’ikan abinci iri-iri, kamar sinadaran bitaman da mineral. Me zai hana a yi mana bayani a kansu da irin aikin kowanne?
Daga Ibrahim, Kura
Amsa: Abincin da muke ci a kowane lokaci yana dauke da sinadarai da dama. Akwai sinadarai guda shida, wadanda dole kowane lafiyayyen abinci a ce yana dauke da su. Duk da haka dai ba kasafai akan samu abincin kowa ya zama yana dauke da sinadaran ba, dari-bisa-dari.
Sinadarin kara Kuzari (Carbohydrate): Shi wannan sinadari a cikin abinci shi ne yake ba mu kuzari, wato karfin yin duk wasu ayyukan ranar. Ana samu a jikin masara, shinkafa, gero, dawa, alkama ko maiwa da sauran kayan hatsi.
Sinadarin Gyarawa da Gina sassan jiki (Protein): Shi kuma wannan shi ne yake gina mana jiki da kara kwarin gabobin jiki, inda aka samu tangarda kamar rauni ko idan wata cuta ta ci sashen, ya gyara. Ana samu a nama, kifi, kwai, madara, wake da sauransu.
Sinadaran Maiko: Wannan shi ke taimaka wa ciki markada abinci, kuma ana ajiye shi a karkashin fata a matsayin teba da kuma cikin hanta a matsayin abinci mai kara kuzari na gaggawa. Wato lokacin da jiki ya bukaci abu mai kuzari cikin gaggawa shi jiki ke narkawa a samu dan kuzari.
Sinadaran Mineral: Su ne irin su Calcium, Potassium, Phosphorous, Magnesium da sauransu, wadanda ke taimaka wa protein aikin gina jiki, su taimaka wa carbohydrate wajen ba mu kuzari, su kuma taimaka wa bitaman yin aikinsu yadda ya kamata. Wato kusan su ’yan aike ne.
Sinadarin Ruwa: Sai kuma goga abokin tafiya, ruwa. Ko ka gan shi ko ba ka gan shi ba, ko ka sha shi zallansa ko ba ka sha ba, akwai dai ruwa a kowane abincin da kake ci, wanda idan babu shi ba rayuwa. Kusan kashi saba’in cikin dari na jikinmu ruwa ne.
Sinadaran Bitamin: Su suka fi yawa. Suna taimaka wa jiki ayyuka daban-daban na yau da kullum, kamar sarrafa shi abincin, taimakawa wajen kashe wadansu kwayoyin cuta, taimaka wa protein gina sassan jiki da sauransu. Su suka fi yawa a sinadaran abinci, shi ya sa aka sa su a rukunnai na A, B, C, D, E da K:
1.    Bitamin na rukunin A: Amfaninsa shi ne kara karfin ido. Yana kuma hana dundumi (ciwon da mutum zai kasance yana gani da rana, amma da duhu ya yi, ya daina gani sosai). Ana samunsa a abinci kamar karas, alayyahu, man kifi, hanta ko gwaiduwa. Hukumar Lafiya ta Duniya ta ba da umarnin sa shi a cikin man gyada da buhun sikari saboda a kara yawan abinci masu dauke da shi.
2.    Bitamin na rukunin B: Wannan rukuni ya kunshi nau’in sinadarai da dama, shi ya sa ake kiransu B compled:
B1 – Wani sinadari da ke kara wa laka ko jijiyoyinmu karko. Ana samunsa a hatsi da shinkafa.
B2 – Wani sinadari da ke taimakawa wajen sarrafa abincin da muka ci. Ana samunsa a kwai da alkama.
B3 – Wanda ke taimakawa wajen sarrafa sababbin kananan halittu na jiki (cells) don maye gurbin wadanda suka mutu. Ana samunsa a kowane irin nama da kayan marmari da hatsi, in banda masara.
Babu bitaman na B4
B5 – Yana taimaka wa jiki sarrafa abinci, kuma ana samunsa a kusan kowane irin abinci.
B6 – Ana samunsa a madara da nama da shinkafa. Ba a samunsa a hatsi ko kayan itatuwa. Yana kara karkon fata da na jijiyoyin laka.
B7 – Ana ci a hanta da gwaiduwa. Yana kara kyau da kyallin gashi da farce.
Babu rukunin B8
B9 (Folic acid) – Ana samu a duk kayan ganye da na marmari. Babu a hatsi da shinkafa. Yana taimakawa wajen sarrafa sababbin kananan halittu na jiki (cells). Wannan ne ya sa ake ba mata masu ciki kari saboda yawan sarrafa kananan halittu na dan tayi.
B12 – Mai taimaka wa lakar da kwakwalwa wajen ayyukanta na yau da kullum, da sarrafa jajayen kwayoyin jini. Ana samu a hanta da kwai da madara.
3.    Bitamin na rukunin C: Amfaninsa shi ne kara karkon dukkan halittun jiki da tsane kitse. Ana samu a gwaba, lemon zaki da na tsami da wasu ganyayyaki.
4.    Bitaman na rukunin D: Wannan sinadari shi ne kadai jikinmu kan iya sarrafawa. koda ce take sarrafa wani bangare, sai rana ta lokacin hantsi ta karasa ragowar. Yana kara karfin kashi da na hakora. Yaran da ba sa shan hantsi kan iya zama gwame, in har ba a ba su madara ko man kifi ba, tunda ana iya samunsa a madara da man kifi.
5.    Bitaman na rukunin E: Yana kara karfin jijiyoyi da kuma kyan fata shi ma. Ana samu a gyada da man gyada, da hatsi. Ana sa shi a wasu man shafawa da sabulun wanka don gyaran fata.
6.    Bitamin na rukunin K: Shi kuma wannan ana cinsa a ganyen alayyahu da kabeji, da kuma hanta. Shi ne kadai bitamin da kwayoyin bacteria da ke cikin hanji ke sarrafa mana. Yana taimaka wa lafiyar jini kada ya tsinke.
Abin lura a nan shi ne duk wadannan sinadarai, Allah Ya adana mana su cikin abinci, ba sai mun nema a wani wuri ba. In dai mutum na da lafiya, to wadanda yake samu a abinci sun ishe shi kiwata lafiyarsa. Wadanda ake kara wa kwayoyin bitamin a asibiti su ne marasa lafiya, wadanda kuma ba su iya cin abinci ko kuma mata masu juna biyu.
Likita akwai maganin da zan sha don rage kiba da tumbi? Shekaruna ashirin a duniya, amma ina da kibar da ta sa girmana ya wuce na shekaruna.
Daga Maryam
Amsa: Ba magani ake sha ba, rage yawan nauyin abinci ake yi (calory). Abincin da suka fi nauyi su ne masu carbohydrate da maiko. Don haka idan kina cin shinkafa faranti guda a lokaci daya, sai ki koma cin rabi, rabin ki maye da kayan ganye. Idan kina cin kosai shida, sai ki koma cin hudu misali, ki kuma matse man, wanda ya rage shi ne naki. Haka dai kowane abinci ki rage, amma ba a tsallake ci, sai dai idan azumi ake. Sai kuma ki nemi daya daga cikin hanyoyin motsa jiki ki lazimta.
Ni ma ina bibiyar nauyina, sai na ga yana tsakanin kilo 90-100. Akwai matsala?
Daga Usman, Funtua
Amsa: Ya danganta da tsayinka. In kai dogo ne sosai ba matsala. Idan kuma tsaka-tsaki kake to sai a rage, ka dawo kilo 70-80. Shi ne daidai na matsakaita.
Likita, tuffa a wane rukunin abinci take? Sa’annan kuma yawan cinta yana kawo matsala ne?
Daga Aminu, Bichi
Amsa: Tuffa na da sinadaran bitaman na rukunin C da sukari, carbohydrate ke nan, da ruwa. Fiye da rabin tuffa ruwa ne.

 

LAFIYAR MATA DA YARA

Amsoshin Tambayoyi

Ina da mata ta haihu a gida kuma ta karu. Za a iya yi mata aiki daga baya? A ba ni shawara.
Daga Sani B. Kaduna
Amsa: A’a, kusan kafin ma a ba ka shawarar, lokacin aiki ko dinke wannan karuwa ya wuce. A likitance duk wata tsaga ko yanka a jikin mutum (in banda yanka a fuska ko a ka) mai bukatar dinki, idan ta wuce awa ashirin ba a yi ba, ta yi kwantai ke nan, domin kwayoyin cuta sun riga sun shiga, sai dai a yi ta wankewa da shan maganin kashe kwayoyin cuta, in an ci sa’a ya hade, amma sai ya dauki lokaci mai tsawo. Yana da kyau dai a je asibiti a ga wurin, kafin ma’aikatan su yanke shawara.
Ko za a taimaka a rubuta min sunan allurar samun haihuwa? An rubuta min kwayoyi a asibiti ba su yi ba. Ina da ’ya’ya hudu kuma ina son kari.
Daga Maman Abba, Bauchi
Amsa: A’a, a ka’ida akwai abubuwan da ba za a iya rubuta miki a wannan kafa ba, sai dai ko ki canza asibiti. Amma ko kin canza asibitin ma duk likitan da kika ce wa kina da yara da wuya ya rubuta miki wasu karin magungunan samun haihuwa, domin an fi rubuta wa wadanda ba su taba haihuwa ba, ko wadanda suka haihu sau daya aka dade ba a kara samun haihuwa ba, kamar wancan bawan Allah na satin da ya gabata, wanda ya auri bazawarar da ta dade ba ta haihu ba.
An yi wa iyalina allurar wata uku ta tazarar haihuwa, amma sai ta nuna min akwai matsala. Ya ke nan?
Daga Saminu, kurgwi
Amsa: Kowace hanya daga cikin hanyoyin na tattare da ’yar matsala, sai an daure, idan kuma ba irin wadda za a daure wa ba ce, sai a tsayar. Amma tunda an riga an yi allurar ka ga ke nan sai an yi kusan wata uku ke nan ana samun matsalar. Ko ma dai mene ne, za a iya samun maganin rage matsalar idan kuka koma asibitin, idan kuma wadda za a iya daurewa ce, ka ga idan wata ukun sun cika, sai a canza dabara.