✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugabar Tanzaniya tana shan suka kan muzanta ’yan kwallon kafa mata

Ta kwatantasu a matsayin masu shafaffen kirji.

Shugabar Kasar Tanzaniya Malama Samia Suluhu Hassan ta sha suka saboda yadda ta siffanta ’yan kwallon mata da suke buga wa kasarta wasan kwallon kafa.

Wakiliyar BBC ta ce Shugaba Samia — wadda ita ce mace ta farko da ta zama Shugabar Kasar — ta kwatanta ’yan matan da masu shafaffen kirji, kuma wadanda suka cika muni, matsalar da ta ce tana iya hana su yin aure.

Shugabar Kasar ta kuma ce ana iya kuskuren wadansu ’yan mata ’yan kwallon a ce maza ne.

Ta yi wadannan kalamai ne yayin wani biki da aka shirya na karrama Kungiyar Kwallon Kafa ta Mata ta Kasar ’yan shekara 23 da suka yi nasarar lashe gasar kwallon kafa ta mata ta Gabashi da Tsakiyar Afirka.

An kuma soki Shugaba Samia kan ci gaba da hana ’yan matan da suka dauki ciki su ci gaba da halartar makaranta.