Shugabar Kasar Tanzaniya Malama Samia Suluhu Hassan ta sha suka saboda yadda ta siffanta ’yan kwallon mata da suke buga wa kasarta wasan kwallon kafa.
Wakiliyar BBC ta ce Shugaba Samia — wadda ita ce mace ta farko da ta zama Shugabar Kasar — ta kwatanta ’yan matan da masu shafaffen kirji, kuma wadanda suka cika muni, matsalar da ta ce tana iya hana su yin aure.
- Juventus za ta maye gurbin Ronaldo da Hazard, Chelsea za ta dauki Jules Kounde
- Matsalar tsaro: Ku kare kanku —kungiyar Kiristoci
Shugabar Kasar ta kuma ce ana iya kuskuren wadansu ’yan mata ’yan kwallon a ce maza ne.
Ta yi wadannan kalamai ne yayin wani biki da aka shirya na karrama Kungiyar Kwallon Kafa ta Mata ta Kasar ’yan shekara 23 da suka yi nasarar lashe gasar kwallon kafa ta mata ta Gabashi da Tsakiyar Afirka.
An kuma soki Shugaba Samia kan ci gaba da hana ’yan matan da suka dauki ciki su ci gaba da halartar makaranta.