Shugabar mata ta Jam’iyar PDP a Jihar Sakkwato, Hajiya Kulu Abdullahi Rabah, wadda aka sani da ’Yar Sardauna ta sauya sheka zuwa APC kwana hudu kafin zaben gwamna da za a gudanarwa a ranar Assabar.
Hajiya Kulu Rabah a takardar da ta aike wa shugaban mazabarta a garin Mai Kujera a karamar hukumar Rabah, ta sanar da shi barin jam’iyar saboda rashin fahimtar da ke cikin PDP, lamarin da a cewarta ya hana ciyar da Jihar Sakkwato gaba.
- An maka dan takarar gwamnan PDP na Katsina a Kotu kan kudin zabe
- Shin har yanzu Kano da Legas na da tasiri ga nasarar dan takarar shugaban kasa?
Kulu Rabah, jim kadan da barin PDP ta bayyana shigarta APC a gaban jagoran Jam’iyar APC a jihar, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko da dan takarar gwamna, Ahmad Aliyu Sokoto.
Jam’iyyar PDP ne dai ke mulkin Jihar Sakkwato a halin yanzu, sai dai a wannan karo ba gwamna mai ci, Aminu Waziri Tambuwal ba ne dan takararta.
Tambuwal ya tsaya takarar zuwa Majalisar Dattawa a zaben da aka gudanar ranar 25 ga watan Fabrairu, amma Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bayyana cewa zaben bai kammala ba.
Gabanin haka, ya yanki tikicin tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar, amma a ranar zaben tan takarar ya janye wa tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar.
A karshe dai Atiku ne ya zama dan takarar shugaban kasa na PDP, amma ya sha kaye a hannun Bola Tinubu na Jam’iyyar APC mai mulki.