Shugabar Matan Shiyyar Arewa maso Yamma ta jam’iyyar NNPP, Aisha Ahmed Kaita, ta yi murabus daga mukaminta.
Aisha, ta bayyana hakan lokacin da ta gana da manema labarai a Kano ranar Talata, inda ta bayyana cewa ta yi murabus daga muƙamin nata bisa raɗin kanta, kuma za ta ci gaba da zama a jam’iyyar.
- Hotuna: EFCC Ta Gabatar Da Jami’in Kamfanin Binance A Kotu
- NAJERIYA A YAU: Yadda Za Ku Gane Daren Lailatul-Ƙadri Cikin Sauƙi
Ta bayyana cewa ta ɗauki matakin ne sakamakon rashin bai wa magoya bayanta muƙamai a gwamnatin NNPP a Jihar Kano.
Ta ce, “Na sanar da shugaban NNPP na kasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ƙudurina na sauka daga muƙamina na shugabar matan shiyyar Arewa maso Yamma.
“Ya tambaye ni ko akwai matsala ko wani abu da ke faruwa, amma na sanar da shi cewar babu komai kuma zan ci gaba da zama a jami’yyar, amma akwai buƙatar na sauka daga muƙamina.”
Ta bayyana cewar za ta ci gaba da yi wa Sanata Kwankwaso biyayya.
Kazalika, ta bayyana cewa za ta ci gaba da kasancewa mai goyon bayan Kwankwaso a dukkanin harkokin siyasar jami’yyun APC, PDP da kuma NNPP.