✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugabar Matan NNPP ta yi murabus kan rabon muƙamai a Gwamnatin Kano

Na sanar da jagorann NNPP na kasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ƙudurina na sauka daga muƙamin.

Shugabar Matan Shiyyar Arewa maso Yamma ta jam’iyyar NNPP, Aisha Ahmed Kaita, ta yi murabus daga mukaminta.

Aisha, ta bayyana hakan lokacin da ta gana da manema labarai a Kano ranar Talata, inda ta bayyana cewa ta yi murabus daga muƙamin nata bisa raɗin kanta, kuma za ta ci gaba da zama a jam’iyyar.

Ta bayyana cewa ta ɗauki matakin ne sakamakon rashin bai wa magoya bayanta muƙamai a gwamnatin NNPP a Jihar Kano.

Ta ce, “Na sanar da shugaban NNPP na kasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ƙudurina na sauka daga muƙamina na shugabar matan shiyyar Arewa maso Yamma.

“Ya tambaye ni ko akwai matsala ko wani abu da ke faruwa, amma na sanar da shi cewar babu komai kuma zan ci gaba da zama a jami’yyar, amma akwai buƙatar na sauka daga muƙamina.”

Ta bayyana cewar za ta ci gaba da yi wa Sanata Kwankwaso biyayya.

Kazalika, ta bayyana cewa za ta ci gaba da kasancewa mai goyon bayan Kwankwaso a dukkanin harkokin siyasar jami’yyun APC, PDP da kuma NNPP.