✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugabar kasar Hungary ta yi murabus kan zargin goyon bayan masu fyade

Shugaba Katalin Novak ta yi murabus kan zargin ta afuwa ga mutanen da kotu ta daure kan laifin fyade ga kananan yara.

Shugabar Kasar Hungary, Hungary Katalin Novak, ta sauka daga mukaminta sakamakon zargin ta da goyon bayan masu fyade ga kananan yara.

Shugaba Katalin Novak ta sanar da ajiye mukaminta ne sakamakon guguwar da ta taso ta zargin ta da afuwa da wasu mutane da kotu ta yanke wa hukuncin sauri a gidan yari bayan kama su da laifin fyade ga kananan yara.

Wannan dambarwa dai ta taso ne lbayan da shugabar ta yanke shawarar yafe wa mataimakin shugaban wani gidan kula da kananan yara, wanda ya taimaka wajen rufa wa shugaban gidan asiri kan fyaden da ya yi wa wasu kananan yara.

’Yan adawa dai ne suka rura wutar wannan ce-ce-ku-ce da ke alakanta shugabar kasar da goyon bayan masu cin zarafin kanan yara a fakaice.

A wata takarda ta ta mika wa fira ministan kasar, Victor Orban, shugaba Novak, mai shekaru 46 ta ce za ta bar aiki a sakamakon fushin da ’yan kasar ke yi da ita kan matakin da ta dauka wanda a ganin ta shi ne dai-dai.

Takardar ta kuma kunshi ban hakuri da neman yafiya a gurin wadanda matakin nata ya fusata, tana mai cewa ta yafe musu ne ba don tana goyon bayan laifin da suka aikata ba.

Jim kadan bayan wannan sanarwa tata, kuma sai ministar shari’a ta kasar Judit Varga itama ta sanar da janyewar ta daga duk wata harka ta siyasa da aikin gwamnati, duk dai kan wannan batu.

Novak dai ita ce mace ta farko da ta fara rike wannan mukami, wanda ta fara tun 2022.